kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa, ta bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana 1 ga Muharram a matsayin ranar hutu, don ba al’ummar Musulmin kasar nan damar gudanar da al’amuran da ke tattare da ranar cikin lumana.
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdulllahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata game da muhimmancin 1 ga Muharram.
Shugaban wanda ya taya daukacin al’ummar kasar nan murnar shiga sabuwar shekarar hijira ta 1436, ya kuma bukaci su kara azama wajen aikata ayyuka nagari, sannan su nisanci munana wadanda za su nisanta su da mahaliccinsu.
Ya yaba wa gwamnatocin jihohi da suka ware ranar farko ta hijiriyya, a matsayin ta hutu, sannan ya bukaci gwamnatin tarayya ta rungumi tsarin don adalci ga Musulmi, kamar yadda take yi a kowane farkon shekarar Miladiyya.
Bala Lau wanda ya yaba da tsarin da aka bi wajen rarraba kayan tallafi na Naira miliyan 73 a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa, jihohin da ke fama da tashe-tashen hankula da kuma Jihar Gombe da kungiyar ta gabatar tare da hadin gwiwar Bankin Ja’iz, ya bayyana cewa daga yanzu kungiyar za ta rika bayyana tsarin aikace-aikacen da take son ta cimma na tsawon shekara a yayin farkon shekarar Musulunci, don tuna wa al’ummar Musulmi zagayowar ranar.