✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iyayen daliban Islamiyyar Tegina sun fara barar kudin fansar ’ya’yansu

Iyayen daliban na bin masallatai da coci-coci neman barar kudin ceto daliban.

Iyayen daliban makarantar Islamiyyar Tanko Salihu da ke garin Tegina a Jihar Neja sun fara barar kudi a masallatai da coci-coci domin karbar fansar ’ya’yansu 136.

Rahotanni sun ce tuni wasu da dama daga cikin daliban suka kamu da rashin lafiya saboda rashin kula da suke samu a hannun ’yan bindigar.

  1. Masu garkuwa sun harbe direba, sun sace uwa da danta a Nasarawa
  2. Rashin tsaro: Aisha Buhari ta bukaci daukar karin jami’an tsaro

Shugaban makarantar, Malam Alhassan Garba Abubakar, ya tabbatar da cewar ’yan bindigar na neman Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansar daliban Islamiyyar.

“Ban jima da yin magana da masu garkuwar ba, sun tabbatar da dukkan daliban na raye, amma wasu daga ciki ba su da lafiya,” inji shi.

Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata wasu ’yan bindiga suka kutsa kai cikin Islamiyyar tare da yin awon gaba da daliban kimanin 136.

Daga bisani dai masu garkuwar sun bukaci a basu miliyan 200 a matsayin kudin fansa, sai dai gwamnatin Jihar Neja ta ce ba zata biya ko sisi ba don ceto daliban.

Tuni dai iyayen daliban suka fara bin masallatai da coci-coci da ke Karamar Hukumar inda suke neman agajin kudin fansar daliban.

A cewar shugaban makarantar, “Yanzu iyayen na zuwa masallatai da coci-coci don barar kudin da za a biya ’yan bindigar, amma abin da aka tara zuwa yanzu bai taka kara ya karya ba.

“Bana cikin kwamitin iyayen da ke neman taimakon, don haka ba zan iya bayyana nawa aka tara kawo yanzu ba,” cewar Abubakar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Alhaji Ahmed Matane, ya ce ’yan bindigar za su iya komai don tabbatar da cewar an biya kudin fansar.

Kazalika, ya jadadda cewar jihar na kan bakarta na kin biyan kudin fansa don ceto daliban.

Sakataren Gwamnatin ya ce Jihar na tattaunawa da iyayen daliban tare da basu tabbacin kubutar da su cikin koshin lafiya.