✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kashe ’yan gudun hijira ta jikkata sojoji a Borno

Mayakan ISWAP sun kashe ’yan gudun hijira uku da jami'in tsaro daya, tare da jikkata sojoji takwas da fararen hula biyar a Borno.

Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe ’yan gudun hijira uku da jami’in tsaro daya, tare da jikkata sojoji takwas da fararen hula biyar a yankin Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno.

Aminiya ta gano cewa mayakan sun harbe ’yan gudun hijira da suka shiga daji neman ice, sannan suka yi wa daya raunin.

Sun kuma harba roka a wani hari inda suka jikkata sojoji takwas da fararen hula biyar.

Wani jami’in tsaron sa-kai na Civilian JTF ya ce wanda ya tsere daga cikin wadanda suka je neman ice ne ya kawo rahoto, aka je aka dauke gawarwakin aka yi musu jana’iza.

Wata majiyar tsaro ta ce sojoji sun kashe mayakan ISWAP da dama amma ba a tantance adadinsu ba.

Ta kara da cewa jami’in Civilian JTF daya ya kwanta dama a musayar wuta.

Majiyar ta ce an jikkata mutum sama da 12 ciki har da sojoji takwas a arangamar a maboyar kungiyar da ke Talala a ranar Talata.

Ta ce jirgin yaki ya garzaya da sojojin asibiti a Maiduguri ranar Alhamis.