✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kai hari garin su Burutai, ta hallaka mutane

Mayakan sun kashe ma'aikata biyu a Kwalejin TY Burutai.

Akalla mutum biyu ne ake fargabar mutuwarsu sakamakon wani hari da mayakan kungiyar ISWAP suka kai garin su tsohon Babban  Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Laftanar-Janar Tukur Buratai mai ritaya.

Mayakan sun kai harin a garin Burutai da ke Karamar Hukumar Biu na Jihar Borno ne da misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin, inda suka dinga barin wuta a kan mai uwa da wabi.

Rahotanni sun bayyana cewa kai harin ke da wuya, sai aka sake tura dakarun soji yankin inda suka yi dauki ba dadi da mayakan na ISWAP.

“A ranar 10 ga watan Janairu, 2022 mayakan ISWAP cikin motoci kusan 10 tare da wasu a kafa sun kai hari garin Burutai.

“’Yan ta’addar sun samu damar shiga Kwalejin TY Burutai inda suka kashe ma’aikata biyu sannan suka kone motoci hudu.

“Sannan sun harba roka da ya tarwatsa wani sashe na kwalejin,” a cewar wata majiyar soji.

Wata majiya ta ce sojoji sun kuma bi bayan mayakan, inda suka tare wasu daga cikinsu suka bude musu wuta, amma kawo yanzu babu bayanin raunatawa ko kashe mayakan.