✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta hallaka mayakan Boko Haram da ke tsere wa sojoji

Mayakan kungiyar tada kayar baya ta ISWAP ta bude wuta kan wasu ’yan Boko Haram da suka tsere wa samamen sojoji a Jihar Borno

Mayakan kungiyar tada kayar baya ta ISWAP ta bude wuta kan wasu ’yan Boko Haram da suka tsere wa samamen sojoji a Jihar Borno.

A baya dai Aminiya ta kawo labarin yadda ambaliya da ruwan wutar da sojojin ke yi wa ’yan Boko Haram din, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga Dajin Sambisa zuwa Gabashin Karamar Hukumar Konduga da ke jihar.

Wasu daga cikin mayakan da suka tseren na kan hayarsu ta guduwa kauyen Cina da ke karamar hukumar ne a lokacin da ’yan ISWAP din suka bude musu wuta.

Da yake karin haske kan lamarin, wani mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin Tabkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce harin sojin ne ya tilasta wa daruruwan ’yan Boko Haram da iyalansu tserewa daga sansanoninsu, don tsira da rayukansu.

Wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta ce: “’Yan Boko Haram din na tafiya ne bisa jagorancin Kwamandoji biyu, kuma sun fi su 100.

“Amma saboda ba su da makamai da yawa da suturar arziki kuma babura biyu kadai gare su, uwa uba sun gabal baita saboda yunwa da gajiya.

“Sannan ga ruwan sama da yayi musu duka, wannan ne ya sanya ISWAP din suka samu galaba a kansu; Amma ba su taba mata da kananan yaran cikinsu ba,” in ji majiyar.

Rahotanni dai na nuna a baya-bayan nan rundunar tsaron hadin guiwa da ta da sojojin sama ta samu nasarar halallaka akalla ’yan ta’adda 250 a jihar.