✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta katse ruwan sha da abinci a Gaza

Gwamnatin Isra'ila ta hana shiga da fita gaba daya, sannan ta katse layin ruwan sha da na lantarki da ma abinci a yankin Gaza.

Gwamnatin Isra’ila ta hana shiga da fita ta kuma katse layin ruwan sha da na lantarki da ma abinci a yankin Gaza.

Ministan Tsaron Isra’ila, Yoav Gallant ya ce sun dauki matakin ne bayan rahoton da hedikwatar sojin kasar ta gabatar, a yayin da ake ci gaba da fada tsakaninta da mayakan Hamas.

Ministan ya ce, “Na ba da umarnin toshe daukacin Gaza, babu wutar lantarki, ballanta abinci ko man fetur da sauransu,” kamar yadda shafin Times of Israel ya ruwaito shi yana cewa.

A nasa bangaren, ministan lantarki, Israel Katz ya ba da umarnin da wata sanarwa cewa “yanke wa Gaza ruwa nan take”.

Umarnin na Katz na zuwa ne ba da jimawa ba bayan Gallant na rufe Gaza, wadda ke samun kashi 10 na ruwan sha daga Isra’ila

A safiyar Litinin Isra’ila ta tababtar cewa ta kai hare-hare sama da 500 a Gaza a cikin dare kan cibiyoyin kungiyar Hamas kuma Islamic Jihad.