✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta dakatar da Ministan da ya bukaci a ragargaza Gaza da nukiliya

Saudiyya ta caccaki Isra’ila kan barazanar amfani da nukiliya a Gaza.

Gwamnatin Isra’ila ta dakatar da Ministan Al’adun kasar saboda kiran da ya yi na amfani da makamin nukiliya domin ragargaza yankin Gaza.

Ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya sanar da dakatar da ministan mai suna Amichay Eliyahu wanda ya bukaci jefa bam din domin hallaka duk wani da ke yankin ciki harda Yahudawan da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su.

Eliyahu wanda ya fito daga cikin kawance masu tsatsauran ra’ayin da ke tare da Netanyahu, ya bayyana matsayinsa ne lokacin da yake amsa tambayoyi a wani gidan rediyo mai suna Kol Barama, lokacin da ya ce bai gamsu da irin matakan sojin da kasar ke dauka ba domin murkushe mayakan Hamas.

Lokacin da dan jaridar da ke hira da ministan ya tambaye shi ko yana bukatar a jefa makamin nukiliya a Gaza domin kashe kowa da kowa, Eliyahu ya bayyana cewar wannan na daga cikin matakan da ake iya zabi.

Ministan na Al’adun Isra’ila ya ce akwai yiwuwar su yi amfani da ‘bama-baman nukiliya’ a Gaza, kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar suka rawaito ranar Lahadi.

Eliyahu, minista na jam’iyya Otzma Yehudit mai tsattsauran ra’ayi, ya ce “daya daga cikin zabin da muke da shi a yakin shi ne mu jefa bama-baman nukiliya a Zirin Gaza,” in ji jaridar Times of Israel.

A yayin da ake hirar, Eliyahu ya nuna “adawa kan bari a shigar da kayan agaji Gaza.”

Da kuma aka tambayi Eliyahu dangane da makomar mutane akalla 240 da aka yi garkuwa da su a Gaza, sai ya ce a lokacin yaki a kan sadaukar da rayukan wasu domin samun nasara.

Ministan ya ce rayukan wadanda aka yi garkuwa da su basu zarce na sojojin Isra’ila da ke cikin yakin gadan gadan ba.

Nan take ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya gabatar da sanarwar dakatar da ministan saboda abinda ya kira manufofinsa da suka saba tunanin halin da ake ciki, yayin da sanarwar ta ce Isra’ila na tunanin kaucewa kai hari a kan Falasdinawan da ba mayaka ba ne.

Tuni kungiyar ‘yan uwa da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su suka caccaki ministan da aka dakatar, inda suka shaida masa cewar dokokin duniya sun haramta amfani da irin wadannan bama bamai masu mummunar ta’adi a kan bil Adama.

Saudiyya ta caccaki Isra’ila kan barazanar amfani da nukiliya a Gaza

Kasar Saudiyya a ranar Lahadi ta yi Allah wadai da kalaman da ministan Isra’ila ya yi na shirin amfani da bama-baman nukiliya kan Zirin Gaza da Isra’ilar yi wa kawanya.

“Kin korar ministan nan take daga gwamnati da kuma dakatar da shi ya nuna tsantsar yadda gwamnatin Isra’ila ba ta mutunta bil adama da da’a da addini da shari’a,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta bayyana.

Jordan ta yi Allah wadai da ministan

Kasar Jordan ta yi watsi tare da Allah wadai da kalaman ministan Isra’ila kan amfani da makamin nukiliya a Gaza.

Kasar ta Jordan ta ce wadannan kalaman da ministan ya yi tunzuri ne domin aikata laifukan yaki.

Zuwa yanzu matakin da sojojin Isra’ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, akalla Falasdinawa 9,970 Isra’ila ta kashe a Gaza, daga ciki 4,800 yara ne kanana, sannan 2,550 mata ne.