✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Iska ta hallaka mutum biyu ta lalata gidaje sama da 750 a Taraba

Ruwan sama mai tafe da iska mai karfin gaske ya yi sanadin mutuwar mutum biyu sannan ya lalata gidaje sama da 750 a karamar hukumar…

Ruwan sama mai tafe da iska mai karfin gaske ya yi sanadin mutuwar mutum biyu sannan ya lalata gidaje sama da 750 a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba.

Iskar ta yi mummunar barna ne a garuruwan Mutum Biyu, hedkwatar karamar hukumar, da Sabon Gida da Tella da Takai da Tisol.

Wasu daga cikin wadanda matsalar ta shafa sun shaida wa wakilin Aminiya cewa mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar iskar a garin Sabon Gida suke.

Wuraren da iskar ta lalata sun hada da masallatai da coci-coci da gidaje da kuma gidajen sayar da man fetur tare da shagunan sayar da kayayyaki.

Wani mazaunin yaknin, Mallam Hassan Yakubu, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa mutane masu yawan gaske ne suka rasa matsuguninsu kuma a halin yanzu wadanda iskar ta lalata wa gidajen na kwana a dakunan karatun makaranta tare da gidajen ‘yan uwa wadanda iskar ba ta yi masu barna ba.

Sarkin Mutum Biyu Alhaji Sani Suleiman ya ce iskar ta yi mummunar barna a masarautarsa inda aka yi asarar miliyoyin Nairori ta fuskar gidaje da kayan abinci da dabbobi.

Sarkin ya yi kira ga gwamnatin jihar Taraba ta taimaka wa wadanda suka yi asara da kudade domin su gyara gidajensu da kuma abinci da magunguna.