Iran ta bayyana cewa komai ya kankama don gudanar da musayar fursunoni da Amurka, wanda zai iya faruwa da gaggawa idan Washington ta so.
Da yake fadar hakan a ranar Lahadi, Shugaban kasar ta Iran ya ce “a cikin ’yan kwanakin da suka gabata, mun cimma yarjejeniya kan musayar fursunoni tsakanin Iran da Amurka.”
- NAJERIYA A YAU: Ko Yaya Mulkin Tinubu Zai Kasance?
- Zulum ya kai wa iyalan masuntan da ISWAP ta kashe tallafi
Shugaban ya karasa da cewa “idan komai ya daidaita a bangaren Amurka, ina ganin nan gaba kadan za mu iya samun sauyi, a bangaren diflomasiyyar Iran,” Hossein Amir-Abdollahian ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin.
Akalla Amurkawa Iraniyawa uku ne ake tsare da su a Iran, ciki har da dan kasuwa Siamak Namazi, wanda ya yi wata hira da ba a buga ba ga CNN daga dakinsa da ke gidan yarin Evin da ke Tehran.
A nata bangaren, Hukumar Shari’a ta Iran ta bayar da rahoton a watan Agusta na tsare ’yan kasar Iran da dama a Amurka, ciki har da Reza Sarhangpour da Kambiz Attar Kashani, da ake zargi da “karkatar da takunkumin da Amurka ta kakaba” kan Tehran.
Tun da yake kasashen biyu ba su da huldar diflomasiyya, an sanya hannu kan yarjejeniyar “musayar kuma a kaikaice” tsakanin Iraniyawa da Amurkawa a watan Maris din 2022, in ji Amir-Abdollahian, yana mai kiranta “na jin kai ne kawai.”
A cikin hirar da CNN ta yi da aka watsa a ranar 9 ga Maris, Siamak Namazi ya yi kira ga Shugaba Joe Biden da ya “sanya ’yancin Amurkawa marasa laifi a kan siyasa” ta hanyar inganta sakin su.
An kama wannan dan kasuwa ne a watan Oktoban 2015 kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari saboda laifin leken asiri.
Haka kuma, an yanke wa mahaifinsa Mohammad Baquer Namazi, mai shekaru 85, hukuncin daurin rai da rai a shekarar 2020 daga hukuncin daurin da aka yanke masa, kuma ya samu damar barin Iran a watan Oktoban 2022.
Sauran fursunonin sun hada da Ba’amurke Emad Sharqi da aka yankewa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari bisa laifin leken asiri kamar yadda kafafen yada labaran Iran suka ruwaito, da kuma Morad Tahbaz, Ba’amurke wanda kuma dan kasar Biritaniya, wanda aka kama a watan Janairun 2018 kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari saboda “kudirin hadin gwiwa” da Amurka”.
Akalla masu fasfo na kasashen yamma 16 da suka hada da Faransawa shida ake tsare da su a Iran.