✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta fara shirin tafiya gasar cin kofin duniya a Afirka ta Kudu

A shirye-shiryen da take yi na tafiya gasar cin kofin duniya da zai gudana a kasar Brazil a watan Yuni mai zuwa,  kasar Iran ta…

A shirye-shiryen da take yi na tafiya gasar cin kofin duniya da zai gudana a kasar Brazil a watan Yuni mai zuwa,  kasar Iran ta kai ziyara Afirka ta Kudu don samun horon da ya kamata kafin a fara gasar.
Iran dai tana daga cikin kasashe uku da za su fafata da Najeriya a gasar cin kofin duniya.  Sauran kasashen sun hada da Ajantina da kuma Bosnina-Herzegobina.
A ranar Talatar da ta wuce ne dai ’yan kwallon Iran din suka sauka a Afirka ta Kudu dauke da ’yan kwallo 11 kuma Kocin nasu ya ce ana sa ran sauran ’yan wasan za su tarar da su kafin nan da karshen mako don cigaba da samun horo.
Iran ta taba haduwa da kasar Ajantina a wani wasa da ya gudana a shekarar 1977 a Madrid da ke Sifen kuma an tashi wasan ne a wancan lokaci da ci 1 da 1.
Tuni Hukumar shirya wasan kwallon kafa a Najeriya (NFF) ta aika wata tawaga zuwa Afirka ta Kudu don ganin yadda ’yan kwallon Iran din ke samun horo.