Mahara da ake zargi ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kona Hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Ebonyi.
An wayi garin Litinin ofishin na ci da wuta bayan a cikin dare ’yan binidgar da ake zargin ’yan IPOB ne sun yi masa dirar mikiya, suka yi musayar wuta da jami’an tsaro kafin su cinna masa wuta.
- Yadda mahara suka kashe ’yan sanda 4 da wasu 44
- An yi wa Buhari ca kan rashin halartar jana’izar Janar Attahiru
Harin na IPOB na zuwa ne kimanin wata biyar kafin Hukumar ta gudanar da zaben gwamnan jihar ta Anambra.
Akalla ofisoshin INEC 10 ne IPOB ta kai wa hari ta kuma kona a Kudu-maso-Gabas, yankin da ta rika kai wa ofisoshin jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati hare-hare.
A ranar Laraba, Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya shaida wa taron gaggawa na Kwamishinonin Hukumar cewa hare-haren da ake kai wa ofisoshin na iya kawo cikas ga babban zaben shekarar 2023.
Ya koka da cewa babu abun da ake ragewa na kayan aikin zabe a ofisoshin da ake kai wa hare-haren.