Babu shakka ina mai ra’ayin cewa idan har Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka kyautata albashin ma’aikata ko shakka babu shirin yaki da cin hanci da almundahana da dukiyoyin kasa zai samu nasara ta yadda za a tsabtace al’amura.
Galibi karancin albashin ma’aikata yana sanyawa a rika barna da dukiyar kasa, sannan a rika wuce gona-da-iri domin neman biyan bukatu da suka shafi zamantakewa ba tare da la’akari da dukiyar kasa ake sata ba.
Ma’aikatanmu na Najeriya gaskiya suna bukatar samun albashi mai kyau lura da yadda abin yake a halin yanzu. Sannan ina matukar jinjina musu saboda juriya da hakurin da suke nunawa dangane da karancin albashin da suke karba wanda ko kadan ba ya isar su balle su yi wani abu da sauran abin da ake ba su.
Bugu da kari na lura akwai rukunin ma’aikata da suke bin gwamnatoci wasu hakkoki nasu inda a wasu lokutan za ka ji ma’aikata suna bin gwamnati albashin wata biyu zuwa uku har ma wata hudu ko fiye da haka wanda hakan ya sanya dole ma’aikaci sai ya yi wasu dabaru kafin ya samu abin da zai ciyar da iyalinsa wanda kuma hakan ba daidai ba ne.
Ina fata Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi za su dubi halin da ma’aikatan kasar nan suke ciki domin gaggauta kara musu albashi ta yadda za a samu cikakkiyar nasara a shirin yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da satar dukiyar kasa.
Allah Ya ba mu lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu, Ya kuma bunkasa tattalin arzikin kasa da na al’umarta.
Alhai Usman dangwari, Kano. 08034003230