✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC za ta yi taron gaggawa kan zaben Adamawa

INEC ta ce azarbabin da aka yi na bayyana Binani a matsayin wadda ta yi nasara ba daidai ba ne.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC za ta yi taron gaggawa a yau Litinin kan dambarwar da ta dabaibaye tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa.

Tun a ranar Lahadi INEC ta umarci duk jami’anta da ke lura da zaben gwamna a Adamawa, da su kama hanyar zuwa Abuja domin yin wani taron gaggawa.

Wannan dai na zuwa ne bayan INEC ta bayyana dakatar da aikin tattara sakamakon zaben gwamna da aka karasa a ranar Asabar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun ana tsaka da tattara sakamakon zaben ne Kwamishinan INEC na Adamawa, Barista Hudu Ari, ya ayyana ’yar takarar gwamnan ta jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin wadda ta yi nasara.

Lamarin ke nen da ya sanya cikin wata sanarwar gaggawa da babban jami’inta kan yada labarai da wayar da kan masu zabe na kasa, Barrista Festus Okoye ya fitar, INEC ta ce matakin da kwamishinan zabe na Jihar Adamawa ya dauka na sanar da wanda ya lashe zaben haramtacce ne, don haka ta ce ba za a yi amfani da shi ba.

Sanarwar ta ce kawo yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa ba.

Hukumar INEC ta gudanar da cikon zaben gwamnan Jihar Adamawa ne a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, bayan ta ayyana zaben da aka yi a makonnin da suka wuce a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP shi ne ke kan gaba bisa alkaluman da INEC ta sanar kawo yanzu, yayin da Aishatu Dahiru Binani ta jam’iyyar APC take bi masa a yawan kuri’u.

Yadda lamarin ya yamutsa hazo

An wayi gari Lahadi a Jihar Adamawa cikin wani yanayi na dakon sakamako da rudani.

Tun da farko dai INEC ta dage aikin tattara sakamakon zaben a ranar Asabar, bayan karbar sakamakon zaben cike-gibi da aka yi cikin wasu tashoshin zabe na kananan hukumomin jihar 20.

A ranar Asabar da daddare, jami’in sanar da sakamakon zabe, ya bayyana sakamakon da aka samu a kananan hukumomi guda goma.

Daga bisani kuma ya dage aikin karbar sakamakon zuwa karfe 11 na safe a ranar Lahadi.

Sai dai da misalin karfe 10 na safe, sai babban jami’in INEC wato Barista Hudu Ari, ya shiga zauren tattara sakamakon zaben a Yola tare da rakiyar wasu sun rufa masa baya, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaben.

Bai dai yi bayani filla-filla na sakamakon da kowacce jam’iyya ta samu da kuma yadda aka ci zaben ba.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa yana gama bayyana nasarar Binani ya kama hanya filin tashi da saukar jirage zai bar gari.

Wannan matakin ya sa INEC ta ce aikin da jami’inta ya yi haramtacce ne.