Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta karyata rade-radin da ke yawo cewa ta shardanta mallakar lambar zama dan kasa ta NIN ga masu neman yin rajistan zabe.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a lokacin da yake sanar da cewa za ta ci gaba da yin rajistar masu zabe daga ranar 28 ga watan Yuni, 2021.
- Mahara sun kashe sojoji sun kona sansaninsu a Neja
- Jirgin yaki da Boko Haram ya bace a Borno
- ’Yan bindiga sun kai wa tsohon Gwamnan CBN, Soludo hari
- Bikin ranar haihuwar Tinubu ya bar baya da kura
“Daga ranar Litinin 28 ga Yuni, 2021 za a ci gaba da rajistar masu zabe a fadin Najeriya, har zuwa rubu’i na ukun 2022. Amma za a fi bayar da muhimmanci ga Jihar Anambra saboda zaben Gwamnan Jihar da za a yi ranar 6 ga Nuwamba, 2021,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa za a dakatar da yin rajistar zabe a Jihar Anambra na dan lokaci a watan Agusta, domin a samu damar kammala shirye-shiryen zaben gwamnan.
A jawabin nasa, ya bayyana dalilan da suka sa aka samu jinkiri wurin ci gaba da rajistar zaben yadda Hukumar ta tsara tun da farko.
Da yake jawabin ga manema labarai a ranar Laraba, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce INEC ta bullo da sabbin tsare-tsare domin kawo wa ’yan Najeriya sauki wajin yin rajistar zabe.
“Nan gaba za mu fitar da bayanai game da sabbin tsare-tsare da muka bullo da su domin samar da aminci da saukaka wa masu yin rajista,” inji shi.