✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta yi sabon Mai Magana da Yawunta

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sayi sabbin nade-nade a sashenta Wayar da Kan Masu Zabe da kuma Yada Labarai. Sakataren Yada…

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sayi sabbin nade-nade a sashenta Wayar da Kan Masu Zabe da kuma Yada Labarai.

Sakataren Yada Labaran Shugaban INEC, Roimim Lawrence  Oyekanmi, a cikin sanarwar ta ranar Talata ya ce Nick Dazang shi ne sabon Darektan Wayar da Kan Masu Zabe, yayin da Andy Ezeani ya zama Mataimakin Darektan Yada Labarai.

Nick Dazang ya yi tsohon Sakataren Gudanarwan hukumar a Jihar Kaduna da kuma hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Zai gaji Oluwole Osaze-Uzzi, wanda ya yanzu yake hutun barin aiki gabanin ritayarsa a watan Oktoba.

Shi kuma Ezeani, tsohon editan jaridar Daily Champion, kuma tsohon Sakataren Gudanarwan INEC a Jihar Ebonyi zai maye gurbin Aliyu Bello, wanda ya zama Sakataren Gudanarwan INEC a Jihar Gombe.

Sabbin nade-naden na zuwa ne gabanin zaben gwamna a jihohin Edo da Ondo da za a gudanar a ranakun 19 ga Satumba da kuma 10 ga Oktoba, 2020.