Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta yi wa jadawalin Zaben 2023 kwaskwarima inda ta kara wa’adin kammala zabukan fitar da gwani da kwanaki shida.
Hukumar INEC ta kara tsawaita lokacin ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyun siyasa 18 da aka yi wa rijista.
- Sauti: Abin da mai juna-biyun da aka sace a jirgin kasa na Abuja-Kaduna ta shaida wa Aminiya
- Muhuyi Magaji ya sami takarar Sanatan Kano ta Arewa a PDP
A yayin taron wanda aka yi a hedikwatar INEC a Abuja, Kwamitin Ba Da Shawarwari Tsakanin Jam’iyyu IPAC, ya nemi a kara wa’adin mako guda ga jam’iyyun domin kammala zabukansu na fidda gwani.
Shugaban kwamitin, Injiniya Yabagi Yusuf Sani ne ya nemi INEC ta tsawaita ainihin lokacin da ta sanya na farko na ranar 3 ga watan Yunin gobe.
Injiniya Yabagi ya yi godiya ga INEC dangane da wannan mataki da ta dauka, yana mai cewa wannan wata dama ce da jam’iyyu za su kammala zabukan fitar da ’yan takara cikin aminci.
Da yake tsokaci dangane da lamarin, Kwamishinan INEC na kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar Kan Al’umma, Mista Fetsu Okoye, ya ce tsare-tsare da jadawalin Babban Zabe na 2023 da aka fitar tun a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2022 yana nan babu wani sauyi.
A cewar Mista Okoye, jam’iyyun sun nemi a tsawaita wa’adin kammala zabukan fitar da ’yan takara da kwanaki 37 zuwa 60, sai dai INEC ta yi iyaka kokarinta na kara kwanaki shida, wanda duk ya wuce haka za a samu tangarda a tsare-tsare da jadawalin Babban Zaben, “saboda haka yanzu babu wani sauyi a game da wannan,” inji Okoye.
“Saboda haka kamar yadda Hukumar ta tsara jadawalin Babban Zabe na 2023, jam’iyyu su na da kwanaki shida kamar yadda suka nema daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Yuni su kammala duk wasu zabukan fitar da ’yan takara sannan su dora sunayen wadanda suka yi nasara da duk wasu bayanansu a shafin Intanet na INEC
“INEC ta yi wa jam’iyyun wannan alfarma ce domin su kammala tattara duk sunaye da bayanan gwanayen takara a shafinta.”