Kwamishinonin Kasa na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sun fara ganawar sirri a kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa mai cike da rudani.
Da farko INEC ta kira taron gaggawa a ranar Litinin amma ta dage gudanar da shi zuwa ranar Talata.
- A fara duban watan Karamar Sallah ranar Alhamis —Sarkin Musulmi
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Zai Faru Idan Aka cire Tallafin Man Fetur
Ana sa ran bayan kammala ganawar sirrin na ranar Talata Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kai, Festus Okoye, zai fitar da sanarwa.
Cakwakiyar zaben Gwamnan Adamawa
A ranar Lahadi ne Adamawa ta dauki zafi bayan Kwamishinan Zabe (REC) na jihar, Barista Hudu Yunus Ari ya yi gaban kansa, kafin a kammala tattara sakamakon zaben, ya sanar cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC ta yi nasara a kan Gwamna Ahmadu Fintiri na PDP.
A kan haka ne Hedikwatar INEC da ke Abuja ta nemi shi Hudu da Jami’in Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Mele Lamdio Mohammed — wanda Hudu ya sanar da sakamakon zaben a bayan idonsa — da su bayyana a gabanta.
Hukumar ta kuma ba da umarnin dakatar da tattara sakamakon sannan ta bayyana ayyanawar da Hudu ya yi a matsayin haramtacce, tun ba shi ba ne ke da alhakin sanar da sakamakon zabe, Mele ne.
Daga nan kuma hukumar kira taron gaggawa da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a zaben na Adamawa zuwa ofishinta na Abuja domin tattauna matsalar a ranar Litinin.
Kafin taron ne a ranar Litinin din INEC ta umarci Hudu Yunus, ya tattara nasa ya bar harabar ofishinta nan take sai abin da hali ya yi; ta mika ragamar ofishin ga Sakataren Gudanarwa na jihar.
Daga nan kuma ta sanar da dage taron gaggawan zuwa ranar Talata inda ake sa ran za a yanke shawara kan makomar zaben mai cike da rudani.
INEC ta gudanar da karashen zaben ne a ranar Asabar, bayan wanda aka gudanar ranar 18 ga watan Maris bai kammalu ba.
Duk da cewa Fintiri ke da rinjayen kuri’u a sakamakon da ke hannu a wancan karo, amma kuri’un da aka soke sun haura tazarar da ya ba wa Binani, wadda ke a matsayi na biyu.
INEC ta soke kuri’u tare da umartar a sake zabe a wasu rumfunan zabe ne sakamakon aringizon kuri’u da kuma rigingimun da aka samu da suka janyo soke zaben na farko a wuraren.