✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC ta sanya ranar bai wa zababbun gwamnoni shaidar lashe zabe

Dokar Zabe ta 2022 ce ta dora mana wannan alhaki.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar lashe zabe ga zababbun gwamnoni a jihohin kasar da aka gudanar da zaben gwamna.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da INEC ta fitar mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Ilimantar da Masu Kada Kuri’a na hukumar Festu Okoye.

A cewarta, sashe na 72 (1) na Dokar Zabe ta 2022, ya dora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar lashe zabe ga zababbun ’yan takara a cikin kwana 14 da yin zaben.

A kan haka ne hukumar ta ce ta saka ranar Laraba, 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan na Maris a matsayin ranar da za ta bayar da takardar shaidar lashe zaben ga zababbun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma ’yan majalisun dokokin jihohi.

Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar lashe zaben ne a harabar ofisoshin hukumar da ke fadin jihohin kasar.

Hukumar zaben ta ce Kwamishinonin INEC na jihohi da ma’aikatan hukumar za su sanar da zababbun takamammiyar ranar da za su karbi takardun shaidar.

A halin yanzu dai an bayyana sakamakon zaben gwamnoni 26 daga cikin 28 da aka gudanar.

Jam’iyyar APC ta samu nasara a jihohi 15, jam’iyyar PDP a tara, jam’iyyar Labour guda daya yayin da NNPP ta lashe Kano.

INEC ta kuma bayyana zabukan Kebbi da Adamawa a matsayin wadanda ba su kammala ba.

A dunkule dai, jam’iyyar APC mai mulki ta sake lashe zababbun gwamnoni bakwai a jihohi 15 da suka hada da Babajide Sanwo-Olu (Legas), Dapo Abiodun (Ogun), Abdul Rahman Abdul Razaq (Kwara), Inuwa Yahaya (Gombe), Mai Mala Muni (Yobe), Abdullahi Sule (Nasarawa), da Babagana Zulum (Borno).

Jam’iyyar ta kuma samu nasarar lashe sabbin ‘yan takara takwas: Umar Namadi (Jigawa), Ahmed Aliyu (Sakkwato), Dikko Radda (Katsina), Uba Sani (Kaduna), Bassey Otu (Kuros Riba), Mohammed Bago (Neja), da Hyacinth Alia (Benuwe), da Francis Nwifuru (Ebony).

A bangare guda, PDP ta samu nasara a jihohi tara da suka hada da gwamnoni biyu da aka sake zaba wato Seyi Makinde (Oyo) da Bala Mohammed (Bauchi).

Hakazalika, an zabi gwamnoni bakwai a wa’adin farko na jam’iyyar adawa. Sun hada Peter Mbah (Enugu), Umo Eno (Akwa Ibom), Siminalayi Fubara (Ribas), Kefas Agbu (Taraba), Caleb Mutfwang (Filato), da Sheriff Oborevwori (Delta).

A wata nasara mai cike da tarihi, dan takarar jam’iyyar PDP, Dauda Lawal, ya kayar da Gwamnan Zamfara kuma dan takarar jam’iyyar APC a jihar, Bello Matawalle.

Hakazalika, Abba Kabir na jam’iyyar NNPP ya doke jam’iyyar APC a Jihar Kano, yayin da Alex Otti na LP ya lashe Abia wadda ta kasance karkashin inuwar PDP tsawon shekaru.