Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta sanar da ranar 18 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar zaben Shugaban Kasa da za a gudanar a shekarar 2023.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoban 2020.
- Ba mu yarda a nada hadimar Buhari kwamishinar zabe ba —Sanatoci
- Za mu ci gaba da rajistar masu zabe – INEC
Sanarwar Shugaban Hukumar ta zo ne yayin da ya ke gabatar da sakonsa na fatan alheri yayin rantsar da kwamitin riko na musamman da zai sake yin bita a kan kundin tsarin mulkin kasa na 1999.
A cewarsa, a yanzu Najeriya tana da kimanin kwanaki 855 kafin babban zaben kasa na gaba.