Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za ta kammala zabukan da ba a karasa ba a kasar.
Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan ISWAP 10 a kusa da garin Buratai
- Kwamandan ISWAP ya kashe mataimakinsa saboda harin da sojoji suka kai musu
Baya ga wannan, a wani sako da hukumar ta kuma wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar ne bayan wata ganawa da ta yi da jami’an hukumar a wannan Litinin din.
Hukumar ta ce sai a ranar Asabar 15 ga watan Afrilun ne za a karasa zabukan gwamnoni da na ’yan majalisun dokokin da ba a karasa ba, sakamakon wasu matsaloli.
Ana iya tuna cewa, INEC dai ta ayyana zabukan gwamnonin jihohin Adamawa da Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba.