Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce za ta kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara cewa ta dawo da jam’iyyar ACD da wasu 22 da hukuamr ta soke rajistarsu.
Kwamishinan wayar da kai da ilmantarwa na INEC Festus Okoye, ya ce, a ranar 29 ga watan Yuni, 2020, Kotun Daukaka kara da ke Abuja, a karar da jam’iyyar NUP ta shigar, ta tabbatar wa hukumar hurumin soke rajistar duk jam’iyyar da ba ta cika ka’idodin Sashe na 225A na Kundin Tsarin mulki ba.
Jam’iyyar NUP ta daukaka kara wanda har yanzu hukuncin na gaban Kotun Koli.
“INEC na fuskantar hukunci biyu masu karo da juna daga Kotun daukaka kara. Daya ya tabbatar mana da ikon soke jam’iyyun na biyu kuma ya haramta cire jam’iyyar ACD da sauran 22 daga jerin jam’iyyun.
“Saboda haka za mu tunkari Kotun Koli ta yanke hukunci karshe kan sabanin hukunci da aka samu”, inji Okoye.
Ya ce a yanzu hankalin hukumar ya karkata ne wajen aiwatar da tsare-tsaren zaben gwamnoni a jihohin Edo da Ondo, a ranakun 19 ga watan Satumba da 10 ga watan Oktoba.