Kwana hudu kafin zaben gwamna da majalisar dokoki ta jihohi, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dakatar da Kwaminshin Zabenta na Jihar Sakkwato, Dokta Nura Ali.
Hukumar ta umarci Sakatariyar Gudanarwar INEC a Jihar Sakkwato, Hauwa’u Kangiwa, ta maye gurbinsa nan take, kamar yadda kakakin hukumar, Dokta Shamsuddeen Sidi ya tabbatar.
- INEC ta cire Alhassan Doguwa daga jerin zababbun ’yan majalisa
- Ka nemi lauyoyi ka nufi kotu —Martanin APC ga Atiku
Sanarwar hukumar a ranar Litinin, dauke da Sakatariyar Hukumar, ta umarci Kwamishinar wucin gadin ta hada kai da Kwamishin INEC na Kasa mai sanya idon kan ayyuka, Farfesa Muhammad Sani Kala, idan bukatar hakan ta taso.
Wasikar ba ta bayyana dalilin dakatarwa ba, amma wata majiya a INEC ta ce matakin ba zai rasa nasaba da matsalolin da aka samu a zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki ta tarayya ba.
Idan za a iya tunawa, zaben shugaban kasa da majalisar dokoki ta tarayya a Jihar Sakkwatto ya yi fama da rikici, lattin zuwan kayan zabe, matsalar na’urar BVAS, sayen kuri’u da sauransu.
Aminiya ta ruwaito cewa zaben shi ne na farko da Kwamishinan da aka dakatar ya jagoranta.
“Kuma ka san zaben Jihar Sakkwao na da wuyar sha’ani, don haka ana bukatar wanda ke da gogewa sosai da zai kula da zaben.
“Ina ganin shi ya sa aka umarci kwamishinan zaben jihar ya koma gefe, a samu masu kwarewa sosai su kula da zaben gwamnan da na ’yan majalisar jihar da za a gudanar,” in ji jami’in.
Tuni hedikwatar hukumar ta turo jami’ai da za su kula da zaben da ke tafe.
Saanarwar ta ce, “An turo Kwamishina na Kasa Manjo-Janar A. B. Alkali da wasu manyan jami’ai hudu zuwa Jihar Sakkwato domin gudanar da zaben gwamna da na ’yan majalisar dokoki ta jiha da ke tafe.”