✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato

’Yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu da Rakuma da Tumaki da Awaki.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su.

Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu.

Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin.

Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu da Rakuma da Tumaki da Awaki.

Hadimin shugaban karamar hukumar ya jinjina wa jami’an tsaro kan gaggauta ɗaukar matakin da suka yi na fatattakar ’yan bindigar tare da ƙwato dabbobi da suka yi awon gaba da su.

Aminiya ta ruwaito cewa mutum biyu da suka samu raunin harbin bindiga suna karɓar magani a babban asibitin Tangaza.

Raka ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren ’yan bindiga ke ƙaruwa a garuruwansu musamman da tsakar rana.

Ya yi kira ga mahukunta da su ƙara ƙaimi don ganin an dawo da zaman lafiya a yankin don samar da ci gaba mai ɗorewa.