Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar.
Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Wannan gargaɗin ya biyo bayan wata sanarwa da ake dangantawa wani mai suna Basharu Altine Guyawa wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba a fannin tsaro.
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yi wannan gargaɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
- Mahara sun yi garkuwa da fiye da mutum 50 a Katsina
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu
Usman ya ce irin wannan kalaman suna iya sanya mutane butulce wa abin da gwamnati da jami’an tsaro suke yi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a jihar.
Ya ce “Ya kamata mutanenmu su guji yin magana da tayar da hankali da kuma siyasantar da matsalar tsaro. A maimakon haka, ya kamata su goyi bayan gwamnati a ƙoƙarinta na neman hanyoyin magance matsalolin tsaronmu na dindindin.
“Gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙurin wani mutum ko ƙungiya na kawo cikas ga ƙoƙarinta ko kuma shagaltar da ita a wannan batun ba.
“Gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro sun kasance suna aiki tuƙuru don maido da zaman lafiya, musamman a yankin gabashin jihar da ke fuskantar ƙalubalen tsaro.
“Gwamnati kwanan nan ta yi wani aiki na haɗin gwiwa a yankin wanda ya samu gagarumar nasara yayin da aka lalata maboyar ’yan bindiga da dama da aka gano tare da kashe ’yan ta’adda da dama a cikin aikin. Bugu da ƙari, an kuma ceto daruruwan waɗanda aka yi garkuwa da su a lokacin aikin.”