✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta dage zaben Sanatan Inugu ta Gabas

INEC ta dage zaben zuwa ranar 11 ga watan Maris.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dage zaben Sanatan Inugu ta Gabas wanda za a gudanar a ranar Asabar zuwa ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne, ya bayyana haka a ranar Juma’a a Abuja, a wajen taron tattaunawa da cibiyar tattara bayanai ta kasa da ke cibiyar taron kasa da kasa (ICC) da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan kisan da wasu mahara suka yi wa dan takarar Sanatan jam’iyyar LP, Oyibo Chukwu.

A cewarsa, za a sake gudanar da zaben ne tare da zaben gwamnoni da na ’yan majalisar jiha da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Ya kuma ce za a iya ci gaba da yakin neman zaben Sanata a yankin har zuwa washegarin ranar zaben.