Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage lokacin gudanar da zabukan cike gurbi a jihohi 11 zuwa ranar 5 ga watan Disamba, 2020.
A zamanta da masu ruwa da tsaki ranar Juma’a, hukumar ta ce ta dage gudanar da zabukan ne saboda dalilan tsaro da wasu dalilai na daban.
A baya hukumar ta dage zabukan cike gurbi na ranar 31 ga wata Oktobo a jihohin Legas, Bayelsa, Imo da Kuros Riba da sauransu sai abin da hali ya yi sakamakon tashin hakanlin da zanga-zangar #EndSARS ya haddasa a sassan Najeriya.
Kwamisha na kasa kuma shugaban kwamatin wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ya bayyana ce wa, hukumar ta gudanar da wani zaman tattaunawa da kwamishinonita ranar 22 ga watan octoba, 2020 kan zabukan cike gurbin aka kuma sanya ranar 31 ga watan Octoba, 2020 a matsayin ranar zaben kafin dage ranar sakamakon kalubalen yanayin tsaro da aka ci karo da shi a fadin kasa a sakamakon zanga-zangar #EndSARS.
Okoye ya ce, yanzu sun sake zama ranar Alhamis, 5 ga watan Nuwamba 2020, idan suka yi duba kan halin yanayin tsaro da yiyuwar gudanar da zabukan cike-gurbin da kayan aiki da ofisoshin da aka lalata yayin zanga-zangar #EndSARS.
Wuraren da zabukan cike gurbin ya shafa sun hada da: Mazabar Sanatan Bayelsa ta tsakiya, da Bayelsa ta Arewa da mazabar Dan Majalisar Wakilai ta Nganzai da ke Jihar Borno da mazabar Bayo da ke Borno da dai sauran su.