Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya dage aikin tattara sakamakon zaben shugaban kasa a matakin tarayya zuwa ranar Litinin.
Farfesa Yakubu, wanda ya bayar da sanarwar bayan kabar sakamakon zaben shugaban kasa na Jihar Ekiti, ya ce za a ci gaba da aikin da misalin karfe 11 na ranar Litinin, inda ake fata kafin nan an kawo sakamakon zaben sauran jihohi 35 da kuma birnin tarayya.
- Kwankwaso ya cinye karamar hukumar Ganduje
- Tsohon Kansila ya doke Mai Ladabtarwa A Majalisar Tarayya
Ya sanar da dage aikin ne jim kadan bayan fara tattara sakamakon zaben a Abuja a ranar Lahadi, a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja.
Kafin dage zaman, Farfesa Mahmood Yakubu ya karbi sakamakon zaben Jihar Ekiti, wanda Kwamishinan Zaben kuma Baturen Zaben jihar, Farfesa Ayobami Salami ya gabatar cewa Bola Tinubu na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a 210,494, Atiku Abubakar na PDP 89,554, Peter Obi na LP 11,397 sai Rabiu Kwankwaso na NNPP kuri’a 264.
A ranar Asabar aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda sa’o’i kadan kafin ranar shugaban hukumar ya ba da tabbacin cewa a wannan karon hukumar za ta fitar da sakamakon zabon a kan kari ba kamar yadda aka yi a baya ba.
Ya kuma tabbatar da hukumarsa ba ta da wata matsala ta bangaren kudi, duk da cewa wasu na fargabar cewa sauyin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi, da kuma rashin sakar wa hukumar kudi a kan lokaci na iya kawo mata cikas.
Idan za a iya tunawa dai, a zaben shugaban kasa na 2019, sai a ranar Talata INEC ta sanar da wanda ya ci, bayan kammala zaben a ranar Asabar.