✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta ayyana zaben Majalisar Wakilai ‘inconclusive’ a Kogi

INEC ba ta sanar da lokacin da za a maimaita zabe a rumfunan da lamarin ya shafa ba

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana zaben Majalisar Wakilai na shiyyar Kabba/Bunu/Ijumu a Jihar Kogi wanda aka gudanar ranar Asabar a matsayin wanda bai kammala ba.

Da yake gabatar da sakamakon zabe a cibiyar tattara sakamako ranar Lahadi, baturen zabe, Dokta Adams Baba, ya ce sakamakon zabe na yankin da lamarin ya shafa ba kammalalle ba ne, duk da cewa dan takarar Jam’iyyar ADC,  Salman Idris, da ya fi kowa yawan kuri’u

Ya ce kuri’un 13,867 da Salman Idris ya samu ba su ba shi cancancantar a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe ba bisa la’akari da dokar zabe.

Ya jaddada cewa adadin kuri’un da aka soke a mazabu guda biyu ya zarce tazarar kuri’un da ke tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa.

Don haka Dokta Baba ya ce, bambancin kuri’un da ke tsakanin wanda ya lashe zaben,  Salman Idris na  ADC, da dan takarar Jam’iyyar APC, kuma Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Kolawole Matthew, bai kai adadin masu zaben da aka yi wa rijista a mazabun da aka soke zaben nasu ba.

Da wannan ya ce zaben ya zama “wanda bai kammala ba.”

A cewarsa, “Dan takarar ADC ya samu kuri’u 13,867 yayin da na APC ya samu 13,605, sannan aka samu bambancinm kuri’a 262.”

Sai dai jami’in bai fadi lokacin da za a maimata zabe a rumfunan da lamarin ya shafa ba.