Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Adamawa.
Ya sami nasarar ce da kuri’a 430,861, inda ya doke babbar abokiyar karawarsa, Sanata Aisha Dahiru Binani, wacce ta sami kuri’a 396,788.
- An dakatar da Kwamishinan ’Yan Sandan Adamawa
- Sallah: Zulum Ya Biya Ma’aikatan Borno Albashin Afrilu
A cewar jami’in INEC mai kula da bayyana sakamakon a Jihar, Farfesa Muhammed Mele, hakan ya biyo bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka yi ne tun a ranar Asabar din da ta gabata.
A baya dai an gaza samun wanda ya lashe zaben a na farko da aka yi ranar 18 ga watan Maris, inda dole INEC ta ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba.
Daga bisani bayan karasa zaben ranar Asabar, Kwamishinan Zaben Jihar, Farfesa Hudu Yunusa Ari, ya yi azarbabin bayyana Binani a matsayin wacce ta lashe shi, duk da a lokacin ba a kammala tattara sakamakon ba.
Sai dai daga bisani hedkwatar hukumar da soke ayyanawar, inda ta dakatar da Kwamishinan sannan ta turo aka karasa tattara sakamakon.