✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC da ’yan sanda sun shirya magudi a zaben Kano —Kawu Sumaila

Mun samu labarin cewa INEC ta hana baki da wasu ’yan sanda domin murde zaben Kano.

Zababben Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya yi zargin cewa Hukumar Zabe (INEC) ta shirya magudi a zaben gwamna da na ’yan majalisun dokoki da ke gudana a jihar.

Kawu Sumaila ya yi wannan korafi ne bayan ya kada kuri’arsa a mazabar Sumaila Gabas a Karamar Hukumar Sumaila da ke Jihar Kano.

Honorabul Sumaila ya bayyana cewa INEC na kokarin hadin baki da wasu jami’an ’yan sanda don yin magudin zaben.

“Daga labaran da muke samu daga wakilanmu, ya nuna cewa Hukumar Zabe na kokarin hadin baki da ’yan sanda don yin magudi a wannan zabe.”

A wannan Asabar din ce dai ’yan Najeriya ke zaben gwamnoni a wasu jihohi 28 da ke fadin kasar.

Zaben na wakana makonni bayan zaben Shugaban Kasa da na ’yan Majalisar Tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

%d bloggers like this: