Jigo a jam’iyyar NNP, Injiniya Buba Galadima, ya ce yana tausaya wa Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau saboda komawarsa jam’iyyar PDP.
Buba Galadima dai na tsokaci ne a kan ficewar Sanata Shekarau daga jam’iyyarsu ta NNPP a wata hirarsa da Sashen Hausa na BBC.
- Jam’iyyarmu na da masu zabe miliyan 22 – LP
- Jami’ar IBB ta umarci malamanta su fice daga yajin aikin ASUU su koma aji
Sai dai ya ce duk da ficewar tsohon Gwamnan na jihar Kano, har yanzu akwai magoya bayansa da yawa da suka zauna a NNPP.
Ya ce, “Dama mun sa ran haka za ta iya faruwa. Amma ina tausaya masa saboda ficewar, saboda bai bi hanya mai bullewa ba.
“Duk jam’iyyar da ya koma yakan yi korafin cewa ba a yi masa adalci. Ina mai tabbatar muku cewa a wannan sauya shekar tasa, kaso 90 cikin 100 na magoya bayansa ba za su bi shi ba, za su zauna a NNPP.
“Babu jam’iyyar da za ta so ta yi asarar kuri’a ko da guda daya, saboda za a iya lashe zaben Shugaban Kasa da kuri’a daya. Ba a son ranmu ya fice ba, amma tun da ya tafi, Allah raka taki gona. Ko da mun ci zabe, ina mai tabbatar maka sai ya fice daga bisani,” inji Buba Galadima.
Ya kuma ce jam’iyyar NNPP za ta rubuta wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bukaci sauya madadin Shekarau din da sabon dan takarar Sanata a Kano ta Tsakiya.
Buba Galadima ya kuma ce a kaf cikin ’yan takarar Shugaban Kasa babu wanda zai samu kaso daya bisa hudu na kuri’un da Kwankwaso zai samu a Arewacin Najeriya a zaben na 2023.