✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina shirin samar da gidauniyar adana ayyukan Shata da na sauran mawaka – Sheme

A kwanakin baya ne marubuci kuma dan jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke kunshe da bunkasasshen tarihin shahararren mawakin Hausa,…

A kwanakin baya ne marubuci kuma dan jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke kunshe da bunkasasshen tarihin shahararren mawakin Hausa, marigayi Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana da shi, inda ya warware zare da abawa na irin fadi-tashin da ya sha wajen samar da wannan littafi mai suna SHATA IKON ALLAH. Mun kawo kashi na daya da na biyu, yau kuma ga karashen tattaunawar:

Ganin cewa marigayi Shata ya rasu bai ga littafin na farko ba balle wannan, yaya dangantakarku take da iyalansa?

Tun farko ina da kyakkyawar dangantaka da iyalin Shata. Farkon mu’amalata da shi ma, ’ya’yan nasa yawanci kanana ne, amma yanzu duk sun girma, sun hayayyafa. Yaran Shata irin su marigayi Alhaji Ya’u Waziri da marigayi Alhaji Bawa Dungun-Mu’azu sun san ni da Shata, don haka kowanensu har gida nake samunsa mu yi hira. Sannan ina da amini a gidan Shata, wato Alhaji Mustapha Sulaiman Shata, wanda da ne ga mawakin, to ya taimaka kwarai wajen bude mini kofofi a farkon fara bincikena.

Bayan rasuwar Shata kuma, sai uwargidansa, marigayiya Hajiya Furera, ta rike ni kamar danta; kowane irin bayani na nema game da Alhaji, za ta ba ni koda a waya ne. Akwai kuma kishiyarta, Hajiya Dije (mahaifiyar Sanusi Shata), ita ma muna zumunci sosai, kuma har zuwa daf da buga wannan sabon littafin, ta taimaka mini sosai. Misali, lokacin da nake neman wani hoto, sai ta tashi takanas daga Funtuwa ta tafi garin mahaifinta, wato Falgore, ta kwaso dukan hotunanta na rayuwarta da Shata, ta ba ni. Da yake Hajiya Furera kuma ta rasu, sai danta, Bishir, wanda ke aiki a Maiduguri ya ba da umarni ga matarsa cewa ta kwaso dukan hotunan mahaifiyar tasa da ke cikin wani buhu, a ba ni. To, ka ga akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da iyalin Shata. Kuma har yau din nan ina kallon kaina a matsayin dan uwansu, tunda ni mai kaunar Alhaji ne irin na har abada. Don haka ina matukar son ganin cewa rayuwar zuriyarsa ta inganta kwarai da gaske.

Wane shiri kake yi game da wannan littafi na Shata yadda zai shiga duniya kuma ya zama wata sila na taskace ayyukan mawakan Hausa, ba na Shata kadai ba?

Shekaru masu yawa da suka gabata, na taba jagorantar wani yunkuri na kafa wata kungiya mai suna Gidauniyar Mamman Shata ko Cibiyar Mawaka Da Kade-Kade ta Mamman Shata, ba domin komai ba sai domin a taskace ayyukan da Shata da sauran mawakan Hausa suka yi wajen adana Adabin Malam Bahaushe. Shugaban kungiyar shi ne Alhaji Hamisu Gamarali Funtuwa, ni kuma Sakatare. Kungiyar ba ta siyasa ba ce kuma ba ta neman kudi ko riba ba. Amma tun tashin farko mun samu matsala, domin wani kuskure da muka tafka. Insha Allah za mu sake zama domin farfado da kungiyar da gyara mata fasali.

Burin kungiyar shi ne ta samar da wani gida, inda za a rika tara dukan wakokin Hausa, ba na makadan zamanin da ba kadai, har da na yanzu, irin su Aminu Ala da Mudassir Kasim da Fati Nijar da Maryam Fantimoti da Yahaya Makaho da Umar M. Shareef da sauransu, ta yadda duk mai nema zai je ya samu. Na yi la’akari da cewa idan wadansu mutane da ke rirrike da wakokin suka shude, to wasu wakokin sun salwanta ke nan. A yanzu haka ma akwai wakokin Hausa da suka bata, sai ka sha wuya kafin ka samu wata wakar.

Wane kira za ka yi ga gwamnati da cibiyoyin ilimi da attajirai da ma al’ummar Hausa gaba daya dangane da Shata?

Kiran da zan yi shi ne, su yi kokari su ga an taskace dukan ayyukan adabi na Malam Bahaushe. A nan, ba waka kadai ba, har ma fina-finai da littattafai da hotuna da sauransu. Wadannan abubuwan su ne ke dauke da tarihin al’adunmu, wadanda zamani ke shafewa a hankali. Ba cewa na yi a kafe kan al’ada ba, domin sauyawa take yi, to amma a rika adana ta saboda ’yan baya su gani kuma su ji yadda kakanninsu suke a da. Misali, yanzu kayan kidan Hausawa da dama sun bace; haka abinci da sutura da magunguna. Ko gidan tattara kayan tarihi ka je ba za ka samu wani abin ba. Yanzu ina hoton Narambada? Babu! Hotunan Dan’anace guda nawa ka gani? Ba su da yawa! Ko Abubakar Imam hotunansa guda nawa ake da su? Ba yawa! Shin akwai ma muryarsa a wani faifai kuwa? Ban taba ji ba! To, hakki ne da ya rataya a wuyan duk wanda zai iya da ya bayar da tasa gudunmawar don adana irin wadannan abubuwa. Haka ake yi a duk kasashen da su ka ci gaba.

 

Bayan fitar da wannan babban kundi kan Shata, me kuma al’umma za su tsimaya daga gare ka a nan gaba?

Ina da wasu shirye-shirye na wasu abubuwan da nake so in yi. Idan har Allah Ya ara mini tsawon kwana da lafiya da lokaci, za a ji ni na sake fito da wani abin.

 

Mun kammala