✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina neman afuwar laifin da na yi wa PSG —Messi

Ina neman afuwa bisa abin da na yi kuma ina jira na ga matakin da kulob din zai dauka.

Lionel Messi ya nemi gafara bisa ziyarar da ya kai Saudiyya wadda ta sa kulob din Paris Saint-Germain ya dakatar da shi daga murza leda har mako biyu.

“Ina neman gafara ga abokaina na kulob dinmu da kuma shi kansa kulob din,” in ji kyaftin din na Argentina a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram da ke da mabiya fiye da miliyan 458.

PSG ya dakatar da Messi ne bayan ya ki halartar atisaye ranar Litinin, kwana guda bayan sun sha kashi a hannun Lorient da ci 3-1 a gasar Ligue 1.

Maimakon haka, dan wasan, wanda sau bakwai yana lashe kyautar Ballon d’Or, ya tafi Saudiyya don yin aiki a matsayin mai tallata harkokin yawon bude idon kasar ba tare da neman izinin PSG ba.

“Hakikanin gaskiya na yi tsammanin za a ba mu hutun kwana daya bayan wasan da muka yi kamar yadda aka yi a makonnin da suka gabata,” in ji shi.

“Na shirya kai ziyara Saudiyya saboda a baya na soke shirin da na yi na tafiya kasar. Don haka haka na kasa sokewa a wannan karo.

“Ina neman afuwa bisa abin da na yi kuma ina jira na ga matakin da kulob din zai dauka.”

Bayanai sun ce zai yi wahala Messi ya sake buga wa PSG wasa, ko da yake hakan ya dangantaka da mataki na gaba da kulob din zai dauka.

Kwangilar da Messi ya kulla da PSG za ta kare a karshen kakar wasan da muke ciki, abin da ke nufin wasa uku kawai suka rage masa ya buga a kungiyar.

Messi ya zura wa kungiyar kwallo 31 sannan ya taimaka aka ci kwallo 34 a wasa 71 da ya fafata a PSG, haka kuma ya lashe Kofin Ligue 1 a kakar da ta wuce.

A bayyane take cewa Messi yana da alaka da Saudiyya, domin ko a watan jiya ya wallafa wani sakon Instagram daga can. Kazalika yana tallata harkokin yawon bude ido na kasar.

A watan Maris, mataimakin shugaban Barcelona Rafael Yuste ya yi ikirarin cewa suna tuntubar Messi da zummar komawa Nou Camp.