Tsohon shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Alhaji Ghali Umar Na’abba, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ya rasu a sakamakon cutar coronavirus.
A wani hoton bidiyo da ya aike wa Kanfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Juma’a, tsohon shugaban majalisar ya ce labarin jita-jita ne da ka iya kawo rudani.
Ya ce yana nan a raye cikin koshin lafiya a Landan, bayan tafiyarsa Birtaniya makwanni 4 da suka gabata.
“‘Yan uwana ‘yan Najeriya ni ne Ghali Na’abba, [tsohon] shugaban Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya a shekarar 1999 zuwa 2003.
“Na ji jita-jitar da ake yayatawa a kwanakin nan cewa na mutu.
“Na yi wannan bidiyo ne domin in tabbatar wa ‘yan Najeriya da ma duniya ina raye cikin koshin lafiya, ina kuma alfaharin kasancewa dan Najeriya sai dai ban ji dadin yadda aka yada jita-jitar ba, amma yanzu ba lokaci ne na daukar fansa ba, ni mutum ne mai kyakkyawar mu’amala da ‘yan jarida, amma yana da kyau mu koyi yadda za mu zauna lafiya da juna.
“Ina nan cikin koshin lafiya a birnin Landan tun makwanni hudu da suka shige, kuma tuni na kammala ayyukan da suka kawo ni, ba don rashin jirgin sama ba, da tuni na dawo gida Najeriya.
“Yanzu haka ina kewar gida, kuma ina takaicin abin da ke faruwa a kasata dangane da cutar coronavirus da yadda ake fama da talauci da mutuwar mutane a jihata Kano,” inji Na’abba.
Daga nan sai tsohon dan majalisar ya yi ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukansu a ‘yan kwanakin nan a Kano.
“Mutane da dama sun mutu a ‘yan kwanakin nan a Kano ciki har da ‘yan uwana; don haka zan yi amfani da wannan dama na isar da sakon ta’aziyyata ga duk wadanda suka rasa nasu a wannan ibtila’in”, inji shi.
A karshe ya mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da yalwar arziki a kasa.