✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina maraba da zuwan Messi da Benzema Saudiyya —Ronaldo

PSG ta tabbatar da cewa Messi zai bar kungiyar a wannan bazarar.

A yayin da ake jita-jitar tafiyar wasu zaratan ’yan kwallon kafa na duniya zuwa Saudiyya, tauraron kungiyar Al-Nassr, Cristiano Ronaldo ya ce yana maraba da hakan.

Babbar gasar kwallon kafa ta kasar Saudiyya ka iya zama “daya daga cikin manyan gasa biyar a duniya” idan har aka dauko manyan ’yan wasa a duniya, in ji Cristiano Ronaldo.

A halin yanzu dai ana jijitar cewa Lionel Messi da Karim Benzema da Luka Modric za su koma murza leda a Saudiyya kuma Ronaldo ya ce yana “maraba” da zuwansu.

Gwarzon dan kwallon duniya har sau biyar ya koma Al-Nassr ne a watan Disamban bara, gabanin kammala wa’adin yarjejeniyarsa da United wadda za ta kare ne a shekara ta 2025.

A halin yanzu Paris St-Germain ta tabbatar da cewa Messi zai bar kungiyar a wannan bazarar, kuma dan kwallon na Argentina, mai shekaru 35 ya kasance jakadan yawon bude ido na kasar Saudiyya.

Ronaldo ya zura kwallo 14 a cikin wasa 16, inda ya taimaka wa kungiyarsa Al-Nassr ta kammala gasar a matsayi na biyu a kan tebur a yayin da Al Hilal ta lashe gasar.