A dai-dai lokacin da jam’iyyu a Najeriya ke kokarin kammala zabukan fid-da-gwani domin mika wa hukumar zabe ta kasa (INEC), sunayen wadanda za su shiga babban zaben 2023, za mu dan yi takaitaccen nazari a kan makomar siyasar dan Majalisar Wakilai mai wakilatar Karamar Hukumar Birnin Kano a Majalisar Wakilai, Sha’aban Ibrahim Sharada.
Sha’aban ya kasance kalilan daga cikin matasa a Jihar Kano da suka samu babbar dama a siyasar Najeriya, musamman idan aka yi la’akari da kananan shekarunsa da kuma mukamin da ya fara da shi wato Mai Taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari kan Harkokin Watsa Labarai.
- An ceto mahaifiyar dan takarar Sanata a Kano daga hannun ’yan bindiga
- Tilas mu maida martani idan Koriya ta Arewa ta harba makamin nukiliya —Amurka
Wannan ta ba shi damar samun takarar dan Majalisar Wakilai kuma ya yi nasara a zaben 2019, duk da irin kalubalen da ya fuskanta a cikin jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Birni.
Samun wannan nasara da Sha’aban ya yi, ta sa ya samu damar kasancewa Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilan Najeriya.
Tabbas wannan matashin dan siyasa ya samu dama fiye da wasu daga cikin takwarorinsa musamman wadanda suka fito daga jihar Kano.
Kamar yadda al’umma ke yi wa siyasar Kano kirari da cewa ‘Siyasar Kano Sai Kano’, babu shakka haka abin yake domin sunan Sha’aban Sharada ya karade da’irar siyasar Kano, musamman a shirye-shiryen siyasa da ake gabatarwa a jihar.
Duk da irin rikicin siyasar da ke tsakanin Sha’aban da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Kwamishina Mukhtar Ishaq Yakasai da tsohon dan Majalisar Dokoki, Dokta Baffa Babba DanAgundi da Shugaban Karamar Hukumar Birni, Fa’izu Alfindiki, amma hakan bai sa gwiwar matashin dan siyasar ta yi sanyi a siyasance ba.
Domin kuwa, tuni ya cika kafafen yada labarai a kan bayyana bukatarsa ta yin takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar APC.
Irin karfin hali da kuma tsiwar da Sha’aban din ke yi wa jiga-jigan jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Birnin Kano, ya sanya ake masa lakabi da ‘Sauro mai hana giwa barci’.
Kuma ga duk mai bibiyar siyasar Kano, ya ga matashin dan siyasar ya tayar da kura a cikin APC, musamman a lokacin da ake shari’a mai nasaba da shugabanci a jam’iyyar.
Tabbas irin yadda kafafen yada labarai na ciki da wajen Najeriya, suka bai wa Sha’aban hadin kai da kuma rawaito irin nasarar da tsaginsu na G7 ke samu a kan Gwamna Ganduje, ya sanya yake ganin babu wani dan siyasa a gabansa a cikin APC.
A daya bangaren kuma, ya tattara wasu matasa a cikin wata kungiya mai suna ‘Fitilar Kano’, da babban aikinsu shi ne kare muradinsa da kuma ganin bukatarsa ta biya ta hanyar tattara masa matasa da ba su horo kan kananan sana’o’in dogaro da kai a wasu daga cikin kananan hukumomi 44 da ke Jihar.
Jami’yyar APC ta fara sayar da fom din takara a dukkanin mukamai, sai aka jiyo wata gamayyar kungiyar matasan da Sha’aban din ya sama wa shirin nan na Gwamnatin Tarayya mai lakabin N- POWER, sun tara kudi kimanin Naira miliyan 50 tare da siya wa ‘Sauro’ din fom din neman takarar Gwamnan Kano.
Wannan ce ta ba shi damar shiga zaben fid-da-gwani tsakaninsa da Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, inda Sha’aban Ibrahim Sharada, ya yi rashin nasara.
Hakan ne kuma ya bai wa tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Muntari Ishaq Yakasai damar samun tikitin takarar majalisar wakilai ta tarayya a APC.
Gabanin fara zaɓen fid-da-gwanin, Sha’aban ya gabatar da wani jawabi na mintuna 12 a gaban Ganduje da duk wani mai ruwa da tsaki na APC a Jihar Kano, inda a nan aka ji sauro din ya tuba daga dukkanin irin tsiwar da ya yi wa manyan jam’iyyar tun daga kan gwamna har zuwa kan Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kano, Fa’izu Alfindiki, tare kuma da shan alwashi a kan zai karbi sakamakon zaben fid-da-gwanin.
Sai dai wani abu mai kama da tufka da warwara da sauro ya yi, shi ne yadda aka jiyo shi ya ki amincewa da sakamakon zaben tare da rubuta wa uwar jami’yyar ta kasa korafi tare da zargin cewa an kashe masa magoya baya tare da jikkata wadansu.
Amma ’yan sanda a Kano sun shaida wa manema labarai cewa babu rahoton rikici a yayin zaben balle a yi maganar hare-hare ko asarar rai, har aka kammala zaben.
Yanzu abin tambaya a nan shi ne; mece ce makomar siyasar Sha’aban Ibrahim Sharada a fagen siyasar Kano?
Ko zancen ’yan duniya ya debi sauro ya wuce matsayinsa?
Buhari Abba Rano, dan jarida sannan mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum daga Jihar Kano.