✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina kan gaba duk da adawar Amurka – Ngozi

Za mu ci gaba a ranar 9 ga watan Nuwamba, ko mai rintsi mu ne a gaba.

Tsohuwar ministan kudi ta Najeriya Dokta Ngozi Okonjo-Iweala ya ta ce har yanzu ita ce a kan gaba wajen zama shugabar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO) duk da adawar da Amurka ke yi mata.

Tsohuwar ministar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter, a ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba, inda ta bayyana farin cikinta da bajintar da tayi a kokarinta na zamo wa shugabar WTO.

Ngozi wacce tsohuwar Babbar Darakta ce a Bankin Duniya, ta ce tayi alfahari da ta zamo ‘yar takara da ta sami kuri’u mafi yawa (164) a tarihin cibiyar kasuwancin ta duniya tun bayan da aka kafa ta shekaru 25 da suka gabata.

“Za mu ci gaba a ranar 9 ga watan Nuwamba, ko mai rintsi mu ne a gaba”, inji ta.

Wani abu da ya dauki hankalin jama’a shine ganin yadda kasar Amurka ke adawar da kasancewar Okonjo-Iweala shugabar WTO duk da samun goyon baya mafi rinjaye da tayi.