Ministan harkokin cikin gida da wasanni na kasar Jamus, Horst Seehofer, ya bayyana goyon bayansa ga dawowar gasar kwallon kafa ta Bundesliga a cikin watan Mayu duk da annobar coronavirus a kasar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa Horst Seehofer ya fadi hakan ne ranar Lahadi lokacin da yake hira da jaridar Bild kwanaki uku kafin hukumomi a kasar su gudanar da wani taro a kan lamarin.
“Na ga tsare-tsaren da Hukumar Kula da Gasar Kwallon Kafa ta Jamus ta yi kuma ya yi kyau; hakan ya sa nake goyon bayan dawo da wasanni a watan Mayu,” inji Mista Seehofer.
Hukumar Kula da Gasar Kwallon Kafa ta Jamus dai ta goyi bayan dawo da wasanni wadanda za a rika bugawa ba tare da halartar ’yan kallo ba a tsakiyar watan Mayu.
Idan hakan ya kasance, Jamus za ta zama kasar Turai ta farko ta da dauki irin wannan matakin.
Ministan ya kuma bukaci a samu fahimtar juna tsakanin kungiyoyin kwallon kafa da ’yan wasa a kan ka’idojinda za a gindaya.
“Idan aka samu wanda ya harbu da cutar a wata kungiya, baki daya kungiyar da ’yan wasa da ma ma’aikatan horaswa za su killace kansu na sati biyu”, inji shi.
Ya kara da cewa ba za a bai wa kungiyoyin wasan wani tsarin gwaje-gwaje na musamman ba duk da bukatar da wasu daga cikinsu suka gabatar cewa a yi wa ’yan wasansu gwaje-gwaje a kai a kai.