✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina gayyatar masu zanga-zanga zuwa Gidan Gwamnatin Kano — Abba

Mun samu labari cewa akwai waɗanda suke shirin fakewa da sunan zanga-zanga su tayar da hargitsi a jihar.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani hargitsi da sunan zanga-zanga ba a jihar.

Gwamnan ya yi wannan furuci ne yayin gabatar da jawabansa ga wakilan ’yan kasuwa, sarakuna, da shugabannin addinai a Fadar Gwamnatin Kano ranar Laraba.

Abba Kabir ya nanata cewa “zanga-zanga babu inda za ta kai mu, amma ina shawartar duk waɗanda za su gudanar da ita a matsayin ’yancinsu na ’yan ƙasa da su tabbatar sun yi hakan cikin lumana.

“Mun samu labari cewa akwai waɗanda suke shirin fakewa da sunan zanga-zanga su tayar da hargitsi a jihar.

“Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatinmu ba za ta lamunci wannan yunƙuri ba.

“Saboda haka ina miƙa goron gayyata ga duk masu zanga-zangar da su zo Gidan Gwamnati inda zan ba su kunnen sauraro kan duk wasu korafe-korafe da suke da tafe da su.

“Ba za mu lamunci duk wani nau’i na kawo hargitsi ko tayar da tarzoma a yayin zanga-zangar ba.

“Ko kaɗan ba za mu yarda da lalata kadarorin gwamnati ko fasa shagunan ’yan kasuwa ba,” in ji Gwamnan.

Ya buga misalai kan ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen kawo manufofi da sauye-sauyen da za su inganta rayuwar al’umma a Jihar Kano.