Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusif Gawuna, ya jinjina wa Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan yadda ya aminta da shi ya gaje shi a matsayin Gwamnan Jihar.
Kazalika, Gawuna ya bayyana yadda Ganduje ya ba da sunan shi a baya don yi masa mukamin Minista.
- Yadda ’yan uwan tsohon dan wasan Ajax suka yi ajalinsa
- Kwallo 4 a bana: Shin PSG ta yi asarar dauko Messi?
Mataimakin Gwamnan ya yi wannan furuci ne a dakin taro na Africa Hall da ke Gidan Gwamnatin Jihar, yayin gabatar da fom din takarar ga masu ruwa da tsaki.
Dan takarar Gwamnan a karkashin inuwar jam’iyyar APC ya bayyana cewa, “Mutane ba su san ni kadai ya rike a cikin mambobin Majalisar Zartarwar Jihar nan 19 daga gwamnatin da ta gabata ba.
“A 2018 Shugaban Kasa Buhari ya bukaci Ganduje ya tura sunan mutum daya don nadi shi mukamin Minista, kuma suna na ya tura. Na haye tantancewar da aka min amma daga baya ba a nada ni ba.
“A wannan shekara ta 2018, ya sake kira na a waya ya ce min ya zabe ni a matsayin wanda ya aminta da shi ya zame masa Mataimaki don ciyar da Kano gaba,” inji Gawuna.
Bugu da kari, Gawuna ya ce ba zai ci amanar Ganduje ba matukar ya dare kujerar Gwamnan Jihar a zaben 2023.
“Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu mun yi aiki tare wanda ya sa na koyi abubuwa masu tarin yawa da suka shafi shugabanci da jagorancin jama’a.
Gawuna, ya kuma ba jama’ar Kano da shugabannin jam’iyyar APC a Jihar tabbacin cewar zai yi aiki tukuru don ganin an kai ga gaci a babban zaben 2023 da ke karatowa.