Masu karatu barkanmu da sake haduwa a wannan mako, yau za mu yi waiwaye ne don yin wata shimfida dangane da batun da muka ce za mu yi kan abin da ya shafi babban zaben 2023 da ke tafe.
Wannan shimfida tana da matukar muhimmanci domin sanin yadda aka faro da yadda abin yake yanzu.
Musamman, za mu mayar da hankali ne a kan manyan jam’iyyu uku da suka fitar da ’yan takararsu, har suka fara rangadi da zaga jihohi domin ganawa da ’ya’yan jami’iyyu da fara yakin neman zabe.
A baya an fitar da mujallar ‘Kunnen Gari’ bayan dogon nazari da wasu fitattu kuma ’yan kishin kasa suka yi don isar da abin da ya dace na ilimi kan yadda lamuran siyasa da zamantakewa ke gudana a Najeriya, ganin yadda kafofin wayar da kai suka gaza a aikinsu ko suka bata aikin, musamman a Arewa.
Hakan ya sa aka fitar da wannan mujalla don ta ilimantar ta kuma zaburar da mutane.
Allah Ya albarkaci mujallar ‘Kunnen Gari’ don ta ci gaba da bambance wa mutanen Arewa gari da tsaki musamman daga shugabanninsu kamar yadda take a duk fitowa tsawon watanni ko ’yan shekaru.
Kalaman tsohon Gwamnan Jihar Neja – mai dauke da rawanin Talba – masu nuna rashin damuwa da kisan Sardauna da tsame hannun marigayi Ojukwu a lamarin, da yanayin da Arewa ta tsinci kanta a yau suka sa dole a yi wannan tambihi.
Tsohon Gwamnan Jihar Neja, kuma tsohon Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa, Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu (Talban Minna), ya yi wasu kalamai da suka sa har muka fara nazari da tunanin anya shi ma ba Ibo ba ne haifaffen Minna kamar Ojukwu (wanda aka haifa a Zangeru ta Jihar Neja), ba kamar yadda ya sha nanatawa cewa shi asalin Basakkwace ne? Kamar yadda muka sani mutanen Jihar Neja da dama asalinsu daga tsohuwar Jihar Sakkwato ne tun daga Yawuri zuwa Kwantagora.
Akwai abubuwan da ba dole ba ne su yi dadi ga wadanda suka dauki wannan matsaya da ya kamata Mai Girma Tsohon Gwamna ya sani kafin, da bayan, kisan Sardauna kafin nuna yiwuwar iya koyi ga Ojukwu a tawayensa.
A yadda tsohon Gwamna ke dauka, Chukwuemeka Ojukwu ya yi bore ne ga Gwamnatin Najeriya don amfanin ’yan kabilar Ibo, bisa zargin danniyar da suke fuskanta daga sauran sassan kasar nan kamar yadda suke ikirari.
Hakika ’yan Arewa irin su Janar T.Y. Danjuma (mai ritaya) da marigayi Janar Murtala Mohammed da wasu tsiraru daga Kudu sun jagoranci kifar da Gwamnatin Janar Aguiyi Ironsi wanda Ibo ne a Yulin 1966.
Kuma wani abu da ya kamata a kara sani shi ne; Ojukwu mutumin Ironsi ne sosai.
Matar Ojukwu ta farko, Njideka Ojukwu, ta ce walimar farko da Ikemba na Nnewi ya je da ita, ita ce ta Ironsi.
Kuma har yau akwai zumunci a tsakanin iyalan biyu.
Karewa ma Ironsi ne ya nada Ojukwu Gwamnan tsohuwar Jihar Gabas.
Amma fa wancan mataki da sojojin Arewa suka dauka, ba son rai suka bi ba.
Ya biyo bayan juyin mulkin 1966 ne wanda a lokacinsa aka karkashe manyan Arewa da masu alaka da su kamar Sardauna da Tafawa Balewa da Birgediya Ademulegun da Kanar Shodeinde da Samuel Akintola da Festus Okotie Eboh da sauransu.
Da farko sojoji ’yan kishin kasa sun dauki hakuri ganin rashin samun cikakkiyar nasara daga ainihin masu juyin mulkin, amma karin girma da Ironsi ya yi ga makasan maimakon hukunta su ya janyo ruruwar fitina, musamman ganin cewa ’yan uwansa ne Ibo.
Wannan ya nuna ashe ruwa ba ya tsami banza.
Bayanai sun nuna cewa a cikin sojoji 25 da ya kara wa girma, uku ne kawai daga Arewa, daya kuma daga cikinsu Bayarbe ne wato daga Jihar Yamma.
A wannan yanayi, Ibo a Arewa ba su bar mutanen yankin sun huta ba; cikin izgili sai suka rika rataye hoton gawar Sardauna cikin jini ga Chukwuma Kaduna a gefe suna cewa “Ga babana maganin babanka.”
Wani mawaki mai suna Celestine Ukwu da ya ga tsananin damuwa na sa ’yan Arewa kuka, har wakar nuna jin dadi ya yi mai taken “Awaki na kuka.” Wai ’yan Arewa ne awaki.
A can Gabas kuwa, ganin an kashe Sardauna a Kaduna kamar an ci yaki ne, sai suka yi ta tsallen murna, in ban da kalilan da suke da zurfin tunani.
’Yan kadan ɗin da suka hango daren da ke tafe sun hada da wani ma’aikacin diflomasiyyar Najeriya a Amurka wato Bernard Odugwu.
A wani littafi da ya wallafa mai suna No Place to Hide: Crisis and Conflicts Inside Biafra, ya ce, “Mutanenmu masu ikirarin kawo sauyi sun tsare manyan Arewa sun yi musu mugun kisa sannan sun kara wa kansu mukamai a soji…to lallai ko ba jima ko ba dade sai irin haka ta faru a kanmu”, har ya kawo wani karin magana na Shakespare mai cewa ‘Uba ba fin uba ya yi ba.’
Duk da zargin da ake yi na cewa Nnamndi Azikiwe na da masaniyar abin da zai faru a waccan rana, amma jin munin abin ya sa shi karaya.
Domin an jiyo shi yana kada baki yana cewa “Kashe manyan ’yan siyasa na wani bangaren kasa irin haka da shugabannin sojinsu zai iya janyo wa kasa bala’i irin wanda ba a taba gani ba.”
Za mu gintse kashi na farko na wannan shimfida a nan sai zuwa mako na gaba za mu dora da wannan bayani kamar yadda muka faro domin haska wa al’umma irin abubuwan da suka faru da irin balahirar da aka sha wanda har yanzu abubuwa ba su koma daidai ba tunda aka kashe Sardauna da sauransu.