Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya amince ya ranta wa kasar Ghana Dalar Amurka biliyan uku domin ta farfado daga masassarar tattalin arzikin da ta fada.
Ana sa ran bashin zai taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar sannan ya takaita yawan tashin farashin kayayyaki a kasar da ke Yammacin Afirka.
- Kotu ta yanke wa matasa 4 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Ekiti
- Majalisa ta ba NNPC mako daya ya kawo karshen wahalar mai a Najeriya
Yanzu haka dai Ghana na fama da tashin farashin kayayyakin da ya kai na kusan kaso 40 cikin 100 da kuma ci gaba da faduwar darajar kudin kasar na Cedi tun farkon wannan shekarar.
A farkon wannan watan nan ne dai wasu jami’an IMF suka ziyarci Accra, babban birnin kasar ta Ghana, inda suka tattauna batun tallafa mata da kawo sauye-sauye a harkokin kudinta.
Sai dai a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata, Ministan Kudin kasar, Ken Ofori-Atta, ya ce Ghana a shirye take ta yi abubuwan da za su fitar da ita daga matsin da ta fada, ta inganta kudinta sannan ta dakile ci gaba da tashin farashin kayayyaki.
Ministan ya ce ana sa ran karbo kudaden daga IMF a farkon shekara mai kamawa.
“Amma muna fatan wannan ya kasance bashi ko tallafi na karshe da za mu nema. Shi ya sa ma wannan shirin zai kasance mai karfi.
Shi ma Babban Jami’in asusun na IMF a Ghana, Stephane Roudet, ya fada cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, “Hukumomin kasar Ghana sun nuna himm wajen farfado da tattalin arzikin kasar tun bayan tafiyar annobar COVID-19.”