✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar rashin yin tsafta da kwalliya ga mata

A kodayaushe ina jin dadin yadda idan na rubuta mukala nake samun wayoyin mutane daga garuruwa daban-daban yadda kowa ke bayyana min jin dadinsa da…

A kodayaushe ina jin dadin yadda idan na rubuta mukala nake samun wayoyin mutane daga garuruwa daban-daban yadda kowa ke bayyana min jin dadinsa da kuma addu’o’i na alheri sannan da yadda ake nuna min ana amfana da abin.   Wannan shi ke rara min kwarin gwiwa wajen sako rubuto abin da zai amfane mu baki daya a duk lokacin da na samu dama.

Akwai masu ba ni shawarwarin a kan a duk lokacin da na yi rubutu a kan wani fanni to in rika daurewa ina ci gaba saboda yana yi musu dadi kuma suna amfana.  Amma a ganina da in dauki fanni daya in ta yin rubutu a kansa, to gara in dauko wani fannin da shi ma za mu karu da shi.  

 Na san wasu za su ce me ya sa a kullum rubutuna ya fi rinjaye ne a kan mata? Dalilin da ya sa na fi karkata a kan mata shi ne kasancewata ’ya mace kuma in a kishin na ga mace ko mata ’yan uwana suna cikin wani yanayi da ke bukatar a wayar musu da kai don su gyara.  Ba don komai na fi karkata a kanmu mu mata ba sai don ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, don ina kishin in ga ‘yar uwata mace a wani hali, kuma a cikin zamantakewa ta aure dole mata mu ne a kasa seai mun fara gyara wa sannan abubuwa za su inganta a zamantakewar baki daya, don wasu matsalolin da yawa daga garemu ne, amma su ma mazan da nasu,  amma fannin da na dauko yau na tsafta da kwalliya kusan ya shafi kowa da kowa ne watau daga matan har mazan domin ita tsafta ko don lafiyar jikinmu yakamata mu tsaya mu lura da ita. Allah Ya datar da mu baki daya.

 Tsafta cikon addini ce, tsafta tana daga cikin imani,  kazanta wata abace da take taka muhimmiyar rawa a wurin wargaza zamantakewa musamman ta aure, domin kazanta ba karamin ragewa mace kima takeyi a idon mijinta ba kuma sh ima mijin tana rage masa tasa kimar a idon matarsa, don kazanta tana haifar da kiyayya a zamantakewa.

Akwai abubuwan da yakamata mu lura da su, mu inganta su a wurin gina tsaftarmu.   Misali wanka, wanki, wanke kai, goge dattin kunnuwa, wanke baki, wanke hannu, yankan farce, da sauransu.

Manzon Allah (SAW) yana cewa Allah Mai tsarki ne kuma Yana son tsarkaka.   Idan mun duba za mu ga addinin musulunci kansa an gina shi ne a kan tsafta saboda fadin Manzonmu (SAW) cewa an gina musulunci ne a kan tsafta kuma babu mai shiga aljanna sai me tsafta.  Hadisai da yawa sun yi nuni a kan bayanin muhimmancin tsafta kuma sun yi nuni da kyamar da Allah (SWT) Yake yi wa mai rashin kula da tsafta.

Jiki yana bukatar tsafta, ko na mutum ko na dabba, don rai ta sami sukuni.   Wannan yana nufin ba za a samu tunani mai kyau tare da kazami ba.

A nan ina so mata su gane cewa muna da daraja da kima dole sai mun tsaya mun lura da abubuwa a cikin zamantakewar aure sannan gidanmu zai gyaru, mu kwato wa kawunanmu ‘yancinmu a hannunmu domin addinin musulunci ya fi kowane addini tausaya wa mace a tarihin dan adam.

Amma abin da ke ban mamaki sai ka shiga gidan mace ka ganshi kaca-kaca,  babu sha’awa, kazanta ta tare tun daga tsakar gidanta da dakunanta da ban-daki har ita kanta.  Ga tulin kayan wanki da wanke- wanke kuda suna bi ko kayan wanki a jibge,  yara kuwa sai ka gan su dukun-dukun, hanci dagaje- dagaje da majina.   Idan ma girki take yi sai ka gan shi a bude ko an bude murfi an bar shi a kasa ana face majina, wannan yana daga cikin abin da maza suka tsana.   Kuma koma wane ne ransa ba zai so ba.   Shin ‘yar uwa ba ki san kina dasa kiyayyarki a zuciyar mijinki ba? Duk kuwa da irin soyyayar da kike ganin yana yi miki? 

Wasu matan ba su dauki kwalliya da muhimmanci ba shi ya sa wasu mazan suke burin kara aure ba don ya fita ya bar ki dukun-kudun cikin dauda da tsami amma a lokacin da ya fita sai ya hadu da wata tsaleliyar budurwa tana karairaya ga shi ta caba kwalliya tana kanshi me kike tunanin zai faru, tilas ya fara saka wa a zuciyarsa zai kara aure. 

Abun lura a nan shi ne, ban ce su mazan ba su da laifi ba, don a wasu lokutan za ka tarar matan ne ke da tsafta amma maigida ya kasance cikin wani irin mummunan yanayi saboda rashin tsafta.  Amma dai abin da nake so mu lura da shi a nan mu mata mu gida ke hannunmu, duk yadda muka so sarrafa maza haka za su bi mu kamar akalar rakumi.

Duk macen da ta iya taku, ta iya kwalliya, ta iya girki, ta iya gyara gidanta ciki da waje, babu shakka za ta samun kan mijinta cikin sauki.  Da zarar ya shiga gidan, ba zai yi marmarin fita ba in ba tare da wani kwawwaran dalili ba, don yana jin dadin zama a ciki.  Ga shi gidansa ya yi fes-fes, ga uwargida ta caba kwalliya, don haka zai ji tamkar yana aljannar duniya ne.

Amma idan mace ta kasance cikin dauda, gidanta da dakinta dikin dauda, da zarar miji ya dawo to zai yi Allah-Alah ne ya bar gidan,.  Wasu ba za su sake waiwayar gidan ba sai cikin tsakar dare lokacin kwanciya, kuma da zarar gari ya waye za ka ga suna hanzarin barin gidan, don wasu ko karyawa ma ba za su iya yi a cikin gidan ba saboda kazanta, sun gwammace su tafi teburin mai shayi ko dakunan cin abinci, su karya a can.

To irin wannan da me ya yi kama?  Yakamama mata mu yi wa kanmu fada, mu sani igiyar aurenmu a hannunmu take, sai yadda muka so juyawa da ita. Don haka ya dace mu yi karatun ta-natsu, don mu samu zaman lafiya mai dorewa a gidajen aurenmu.

Da fatan za mu kiyaye, Allah Ya taimake mu.

Don neman karin bayani ko shawara za a iya samun Saddika Habib Abba a 09097438402