✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ilimin zamantakewa zai magance kalaman batanci – CITAD

Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci gaban Jama’a (CITAD) ta bukaci gwamnati ta bunkasa koyar da darasin ilimin zamantakewa a makarantu saboda alfanun da yake da…

Cibiyar Fasahar Sadarwa da Ci gaban Jama’a (CITAD) ta bukaci gwamnati ta bunkasa koyar da darasin ilimin zamantakewa a makarantu saboda alfanun da yake da shi wajen magance kalaman batanci a tsakanin jama’a. 

Babban Jami’in Cibiyar CITAD, Isah Garba ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka saba yi duk wata game da yaki da kalaman batanci.

Malam Isah Garba, ya ce da mutane sun fahimci bambance-bambancen da ke tsakanin addinai da al’adun al’ummar kasar nan da ba su tsoma kansu ga furta kalaman batanci ga junansu ba. “Duk lokacin da muke gudanar da bincike sai mu gano cewa akwai karancin fahimtar da jama’a ke da ita a fannin ilimin zamantakewa, wanda hakan ke sa suke su furta kalaman batanci ga junansu. Don haka muna kira ga gwamnati ta bunkasa koyar da darasin ilimin a makarantu don ya zama hanyar datse wannan mummunar dabi’a ta jifan juna da kalaman kiyayya,” inji shi.

Malam Isah ya ce akwai bukatar gwamnati ta mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin da za su kawo karshen wannan abu cikin hanzari. Kuma a rika wayar wa jama’a kai dangane da hadarin da ke cikin kalaman batanci da yadda suke jawo matsala ga zaman lafiyar kasa.

Malam Isah ya ce jami’ansu da suka bi kafafen sadarwa na zamanin sun gano cewa a watan Agustan da ya gabata an samu kalaman batanci 816 da aka karkasa su kan irin matsayinsu. “Kashi 18.4 sun fi kowane muni, sai kashi 77.3 masu dama-dama sai kashi 4.4 masu saukin nuna kiyayya,” inji shi.

Sai ya yi kira ga jama’a su rika nuna juriya da kawar da kai daga masu kalaman batancin.