Fitaccen malamin Islaman nan mazaunin Kaduni’a, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce babu adalci a yadda ilimi ke gagarar ’ya’yan talakawa a Najeriya, amma shugabannin siyasa na yawo a jiragen kashin kansu na alfarma.
Gumi ya ce Najeriya ta zama wata irin kasa wadda babu adalci, inda hatta fannin shari’arta ya yi rauni ya kuma rasa kadarinsa.
- Ya kashe makwabcinsa don gudun biyan bashi
- Saudiyya ta ba da tallafin Dala miliyan 10 ga ’yan gudun hijirar Ukraine
Malamin ya yi wadannan kalaman ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron gina zaman lafiyar kasa da aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno, a matsayin wani bangare na sake sada tubabbun ’yan Boko Haram da al’umma.
Ya ce, “Duk mai ra’ayin ganin zaman lafiyar kasarmu, mun samar masa da dakarun da zai yi amfani da su.
“Don haka me ya sa muke barin ’ya’yanmu babu ilimi? Me ya sa ilimi bai zama na kowa ba? Me ya sa muka bar al’ummarmu cikin talauci?”
Haka nan, Gumi ya soki lamirin yadda wasu shugabannin siyasa ke shawagi a jiragen sama na kansu duk da halin da kasa ke ciki.
Ya ce, “Wasu ’yan Najeriya na ta shawaginsu a jiragensu, yayin da kuma wasu ’yan kasar ba su ma da abinda da za su tura ’ya’yansu makaranta ba. Akwai rashin adalci a nan.
“Idan kuma ka dubi tsarin shari’a, nan ma babu adalci. An dagula sha’anin gudanarwa.
“Don haka yaran a zube suke ta yadda kowa zai iya amfani da su,” in ji malamin.