Alhaji Abdulrahman Lawal wani fitaccen mai sana’ar kiwon kaji ne a jihohin Bauchi da Filato ne. Ya tattauna da Aminiya inda ya yi bayanin yadda ya fara kiwon kaji da matsalolin da ya fuskanta da kuma nasarorin da ya samu.
Aminiya: Za mu fara da tarihin rayurwaka?
Abdulrahman Lawal: Assalamu alaikum, an haife ni a garin Jos a shekarar 1954, amma asalin iyayena mutanen Jihar Oyo ne. Na yi karatu a Jos da kuma Legas.
Aminiya: Yaya ka fara sana’ar kiwon kaji?
Abdulrahman Lawal: Kafin in fara sana’ar kiwon kaji, na fara ne da sana’ar gyaran kayayyakin wutar lantarki kamar rediyo da sauransu, daga baya na koma sana’ar wanke hotuna. Ni ne mutum na farko da ya fara bude wajen wanke hotuna masu launi a Arewa. Na bude wurin a shekarar 1976 a garin Jos. Daga nan a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa na mulkin soja Janar Muhammad Buhari, sai aka sanya lasisi kan kayayyakin da muke amfani da su wajen wanke hotuna. Hakan ya sa muka samu matsalar shigo da kayayyakin aikin wanke hotunan daga waje, a lokacin gwamnati ta fi ba harkokin noma muhimmanci. Idan muka nemi a ba mu lasisin shigo da kayayyakin wanke hotuna, ba za a ba mu ba. Amma Idan muka nemi a ba mu lasisin shigo da kayayyakin aikin gona, sai a ba mu fiye da abin da muka nema. Wannan shi ne ya jawo ra’ayina na fara jiwon kaji har na bude gonar kiwon kaji mai suna Yankari Farms a shekarar 1986 a karamar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi. A lokacin aka ba ni lasisin shigo da kayayyakin aikin gona, na tafi Turai na sayo kayayyakin aikin kiwon kaji, daga nan muka fara aiki.
Aminiya: Wadanne matsaloli ka fuskanta a wannan sana’a?
Abdulrahman Lawal: Matsala ta farko da na fara fuskanta a wannan sana’a ita ce, a lokacin da na bude wannan gona, akwai kayayyakin da muka yi oda daga Turai, sai ya kasance wadansu daga cikin wadannan kayayyaki ba su samu shigowa Najeriya ba saboda matsalar jiragen da ke shigowa Najeriya, a lokacin babu jiragen da za su zo Najeriya sosai. A karshe muka samu wani jirgin da ya dauko mana kayayyakin, amma sai ya samu matsala a Ghana, maimakon ya karaso Najeriya sai ya wuce Afirka ta Kudu, saboda wannan matsala da aka samu, sai aka sauke mana kayanmu a can. Muka rika wahala a karshe muka yi asararsu. Kudinsu ya kai sama da Naira miliyan 10.
Sannan a shekarar 2006 muka sake samun wata matsala a wannan gona, inda aka gano cutar murar tsuntsaye a wannan gona, aka kashe mana kajinmu duka. A lokacin muna da kaji sama da dubu 100. A nan arewa babu wanda ya kai mu asara a lokacin da annobar ta barke. Kuma a Najeriya babu inda aka kashe kaji kamar a wannan gona. A lokacin gwamnati ta ba mu diyyar iyakar kajin da ta kashe, ta kashe mana kaji dubu 58, ba ya ga wadanda suka mutu kafin su zo. Kajin da ta kashe ne kawai za tA biya diyyarsu, kuma sun biya diyyar Naira 250 kawai kan kowace kaza. A lokacin kudin da ake sayar da ’yan tsaki ma ya kai kusan Naira 200 kowane daya.
Mun mika al’amarinmu a wurin Allah, inda bayan faruwar annobar murar tsuntsaye, mun sake zuba kaji dubbai sau uku suna mutuwa. Amma da taimakon Allah muka sake farfadowa har zuwa yanzu muna samun nasara.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu a sana’ar kiwon kaji?
Abdulrahman Lawal: A gaskiya mun samu nasarori masu tarin yawa a wannan sana’a. Domin mun fara wannan sana’a da kaji kamar guda dubu 5, amma kafin wannan annoba ta murar tsuntsaye ta zo muna da kaji sama da dubu 100, a lokacin muna da ma’aikata 150. Amma yanzu akalla ma’aikatanmu sun kai mutum 50. Muna da reshe a garin Narabi (karamar Hukumar Toro), wadda muke son mu rika fitar da ’ya’yan kaji wadanda za mu rika kawo su Toro don sayar wa jama’a.
Aminiya: Wace gudunmuwa sana’arka ke ba Najeriya?
Abdulrahman Lawal: A gaskiya wannan sana’a tana ba da gudunmawa da dama wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan. Ka ga takin da masu kiwon kaji suke fitarwa, a yanzu manoman kasar nan da dama suna amfani da shi fiye da takin zamani, kasancewar yana raya kasa sabanin takin zamani da ke kashe kasa.
Bayan haka kwan da muke fitarwa suna zuwa garuruwa da dama a kasar nan har da kasashen waje. Wannan ya kawo bunkasar harkar kasuwanci a kasar nan. Haka kuma gidajen kaji suna dibar ma’aikata suna yi musu aiki a gonaki, kuma ta haka za ka ga su ma sun iya wannan sana’a .
Ka ga wadannan abubuwa sun nuna cewa wannan sana’a tana taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma. A kullum nakan fada wa mutane cewa idan da za mu rike noma musamman a nan arewa sai mutanen kudu sun zo sun yi leburanci a Arewa. Kudin man fetur ba ya shiga hannun talaka, kudin noma ne yake shiga hannun talaka. Da kudin noma talaka yake sanya ’ya’yansa a makaranta da gina gida ya yi aure ya sayi mota da sauransu, amma kudin man fetur fa?
Ba maganar gyaran hanyoyin mota ko samar da wutar lantarki ne ke damun talakawa ba. Inganta noma shi ne ya damu talakawan Arewa. Idan aka inganta noma talakawa za su samu kudin da za su sayi jannareto ya biya wa ’ya’yansa kudin makaranta da sauransu. Don haka ya kamata gwamnonin jihohin Arewa su bude dazuzzuka masu fadi na kamar kilo mita 100, su share, su ba matasa, sannan su ba su kayayyakin aikin noma kamar yadda ake yi a kasashe irinsu China, idan aka yi haka za a samu biyan bukata.