✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan na ci zabe zan kammala aikin hakar man Kolmani —Tinubu 

Tinubu ya lashi takobin karasa manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Buhari.

Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, ya ce idan ya ci zabe zai tabbatar aikin hako man fetur na garin Kolmani da ke Jihar Gombe bai tsaya ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin yakin neman zabensa a Jihar Gombe, inda ya ce muddin aka zabe shi gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen kammala aikin.

“Zan tabbatar gwamnatina ta dora kyawawan ayyuka daga inda Shugaba Muhammad Buhari ya tsaya,” in ji Tunubu.

Tinubu, ya kuma yaba wa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na gina gandun masana’antu a garin Dadin Kowa a jihar, wanda zai samar wa dinbim al’umma aikin yi.

A nasa jawabin a filin taron, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, cewa ya yi APC jam’iyya ce da ta kuduri aniyar ci gaba da dorawa kan ayyukan raya kasa da ta ke gudanarwa don ci gaban jihar da ma Najeriya baki daya.

“Zaben Tinubu da Shettima, zabe ne na ci gaban Najeriya, hakan zai taimaka na kara samar da wasu ayyukan raya kasa,” a cewar gwamnan.

Tinubu na ci gaba da shan alwashin kammala ayyukan da gwamnatin Shugaba Buhari za ta bari ba ta kammala ba.