✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IBB ya tafi Jamus ganin likita

Ya tafi ne ranar Asabar don ganin likitocinsa kamar yadda ya saba

Tsohon Shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya tafi kasar Jamus domin likitoci su duba lafiyarsa.

Kakakin tsohon Shugaban, kuma makusancinsa, Alhaji Mahmud Abdullahi ne ya shaida hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Minna, babban birnin jihar Neja, ranar Litinin.

A cewarsa, “Kafin tafiyarsa, ba mu tattauna da maigidan nawa kan inda zai tafi ba da kuma me zai kai shi can kafin ya bar Najeriya.

“Amma na san lokacinsa na ganin likita ya yi, saboda ya kwana biyu bai je ba.

“Saboda hakan, na san ya tafi Jamus ne ranar Asabar domin ya ga likita kamar yadda ya saba,” in ji Alhaji Mahmud.

Sai dai ya ce ba zai iya bayar da cikakken bayani a kan tafiyar ba saboda bai tattauna da IBB ba kafin ya bar kasa.

Amma ya tabbatar wa al’umma cewa babu wani abin fargaba saboda ganin likitansa ya je yi kamar yadda ya saba yi lokaci-lokaci. (NAN)