Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993.
Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne.
Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe zaɓen 12 ga watan Yunin 1993.
- Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria
- ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’
Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to Myself” wanda aka ƙaddamar ranar Talata a Abuja.
Fitattu daga cikin mahalarta taron ƙaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi da takwaransa na Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe da sauransu.
A cikin littafin mai shafi kimanin 500 ya mayar da hankali ne kan rayuwar marubucin tun daga ƙuruciya har zuwa gwagwarmayar siyasarsa daga jamhuriya ta biyu kawo yanzu.
Abin da Sule Lamiɗo ya faɗi
A wani babi mai taken “Matsayata kan rushe zaɓen 12 ga watan Yuni”, Sule Lamiɗo ya musanta dalilin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa mai suna “A Journey in Service” a matsayin dalilin da ya sa ya rushe zaɓen watan Yunin 1993.
Bayan kammala ƙaddamar da littafi, marubucin ya yi wa BBC Hausa ƙarin bayani dangane da haƙiƙanin abin da yake nufi a babin kamar haka:
“A littafin Babangida ya ce Abiola shi ya ci zaɓe. A gaskiya shi ne ya ci zaɓen. Yanzu hujjar sokewa kuma wani abu ne daban.
“Amma ni abin da ya gaya min cewa shi ne dalilin da ya sa ya soke zaɓen shi ne saboda Abiola yana bin Najeriya bashin kuɗi naira biliyan 45 saboda haka idan ya ba shi wannan mulki to zai amfani da mulkin ya biya kansa kuma a lokacin nan ƙasar ba ta da wannan kuɗin da za ta biya shi, shi ya sa ya soke zaɓen.
“Kenan Abiola ya ci zaɓen amma an zalunce shi an hana shi sannan kuma ga kuɗi yana bi ba a biya shi ba.
“Idan ana so a yi adalci tunda mutumin nan ya mutu to kuɗin da yake bi naira biliyan 45 kamar yadda Babangida ya gaya min shi ya sa ya soke zaɓen nan to a ba wa iyalan Abiola, a biya su kuɗinsu. Shi kenan daga nan komai ya ƙare kenan.”
“Shi ya sa nake faɗa wa Tinubu cewa ya kamata maganar June 12 a ƙare ta. Saboda haka a biya wannan bashin na naira biliyan 45 ga iyalansa. Shi kenan magana ta ƙare.”
Abin da IBB ya faɗi a littafinsa
Janar Ibrahim Badamasi Babangida a littafin nasa mai suna “A Journey in Service” ya amince da cewa Cif Mashood Abiola ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar SDP, shi ne ya lashe zaɓen 1993 da ya rushe.
Duk da dai Janar ɗin ya ɗauki alhakin rushe zaɓen amma ya ɗora laifin a kan wasu manyan sojoji da ke aiki ƙarƙashin tsohon hafsan hafsoshin lokacin, Janar Sani Abacha cewa su ne suka rushe zaɓen ba tare da “izinina ba”.
To sai dai littafin na IBB ya janyo martani daga iyalai da ’yan uwan Janar Sani Abacha inda suka yi watsi da zargin.
“Yana da muhimmanci in bayyana cewa Janar Sani Abacha ba shi ba ne shugaban ƙasa ko kwamandan dakarun Nijeriya a lokacin da aka rushe zaɓen 12 ga Yuni ba.
“Kuma an yanke hukuncin soke zaɓen ne ƙarƙashin mulkin Janar Ibrahim Babangida wanda a lokacin shi ne shugaban mulkin soji kuma shi ke da ƙarfin iko a, hakazalika shi ke da alhakin dukkanin ayyukan da gwamnatinsa ta yi,” in ji wata sanarwa da iyalan Abacha suka fitar.