Kodinetar kungiyar I-Nigerian ta kasa Ada Stella Apiafi ta bukaci ’yan Najeriya su kaunaci juna, sannan su rika kishin kasarsu.
Kodinetar ta bayyana hakan ne a lokacin da take yi wa ’yan jarida jawabin sakamakon cika shekara 54 da Najeriya ta yi da samun ’yancin kai a Abuja shekaranjiya Laraba.
Ta ce: “karfin Najeriya ya danganta da yadda ’yan Najeriya ke kishin kasarsu ne da kuma yin aiki ga kasa duk da bambancin yare da al’ada da addini da kuma yanki, duk da cewa an samu matsalolin da suka haifar da barazana ga dorewar kasa, amma ya kamata a hada kai don a samu Najeriya mai dorewa.”
Ta ce zaben shekarar 2015 na karatowa don haka ta bukaci a yi ingantaccen zabe, sannan masu zabe su guji zaben tumun dare don a samar da kyakkyawan canji a kasa. “Don haka ina kira ga ’yan siyasa da su sanya kishin kasa a ransu a lokacin da suke kamfen, ko lokacin zabe ko idan sun samu nasara.”
“Ya kamata mu guji yin kalaman da za su bata wa kasarmu suna, mu fahimta yadda muke magana haka duniya za ta rika kallonmu. Tun da muka shiga shekarar 2014 aka samun tarzoma da tashe-tashen hankula, wadanda suka jawo asarar rayuka da dukiya, hakan ya sanya jami’an tsaro suke iya bakin kokarinsu ba dare ba rana don tabbatar da doka da oda, don haka ya zama dole mu fahimci irin sadaukarwar da suke yi, sannan ya kamata mu rika yi musu addu’a.” Inji ta.
Kodinetan kungiyar na Arewa Aminu Abubakar ya shawarci ’yan Najeriya su rika yi wa shugabanni addu’o’i don a samu shugabanci nagari.
‘I-Nigerian’ ta bukaci ’yan Najeriya su rika kishin kasa
Kodinetar kungiyar I-Nigerian ta kasa Ada Stella Apiafi ta bukaci ’yan Najeriya su kaunaci juna, sannan su rika kishin kasarsu.Kodinetar ta bayyana hakan ne a…